GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Magani 10 Da Ganyen Kurna Da Diyanta Ke Yi A Jikin Dan Adam

Magani 10 Da Ganyen Kurna Da Diyanta Ke Yi A Jikin Dan Adam

37

- Advertisement -

Kasancewa kusan kashi 95 na magunnan da muke ta faman kashin kudi muna saye a shagunnan saida magani waton a chemist da asibitoci akan hada su ne da tsirran itatuwan da tun tuni Allah ya huwacewa kasarmu su,sai dai kawai ilmin kimiya na sanin tasirin sinadirran wadannan itatuwan da yanda ake bincike akan su da kuma hada magani dasu ne ya karamta ga mutanen mu.

 

Kurna wacce muka sani a kasar Hausa na daya daga cikin itatuwan da har a kasar China,India da korea ana amfani da ita dan yin maganin wasu ke6a66un cututtuka.

 

Karanta: An Rabawa Makarantun Fulani Makiyaya Kayayyakin Koyo Da Koyarwa

A kasar korea suna kiranta da suna Korean dates(korean jujuba) waton dabinon korea,haka a kasar India(Indian jujuba) sai a kasar China (Chineese dates).

Bishiyar Kurna nada tsayi da ganye launin kore,tana haifuwar diya masu zaqi dake kumshe da sinadirran da ke samarda karfi ga jiki da inganta lafiya da kuma karfafawa jiki kwarin guiwar yaki da kwayoyin cutuka.

 

Rabin kofi na ruwan danyun diyan kurna (fresh raw jujuba fruit) na daukeda wasu muhimman sinadirai kamar haka : sinadiran calories 76 da grams 20.2 na carbohydrates da grams 1.2 na protein da kuma gram 6.9 na Vitamin C,da milligrams 250 na potassium da niacin da su Vitamin B6 da copper da manganese da sinadiran Iron da sauransu.

 

Karanta: Ya Yi Gunduwa-Gunduwa Da Gwaggonsa Kan Zarginta Da Maita

A kasar korea sun maida shan shayin kurna yanda kasan al’adar shan ataye a kasar Nijar dama wasu yankuna a Nigeria.wannan baya rasa nasaba da yanda suka san alfanonsa.

Sai dai kuma kurna na kawo jinkirn samun juna biyu dan haka mai bukatar samun haihuwa yala mace ko namiji to kada ya sha kurna.

 

Ga jerin magunna goma da kurna ke yi kamar haka :

1.Tana kashe kwayoyin cutar ciwon daji waton cancer.
A wani bincike da wata cibiyar magani dake a kasar Iran mai suna Vaccine and serum Research Institute ta gudanar ta gano cewa diyan kurna busassu(dried jujuba) na kashe kwayoyin ciwon daji(anti cancer cells) wanda tuni suka sanya ta a jerin itatuwan da ke maganin ciwon daji.

 

Karanta: Rigimar Kudi Ya Sa An Cafke Wasu ‘Yan Luwadi 3 A Katsina

 

2.Kurna na maganin damuwa da rashin samun wadataccen bacci da rashin natsuwa.masu bayarda maganin gargajiya na kasar China suna da yakinin haka domin sun jarraba kuma sun dace wanda hakan ya basu damar maida kurna ta zamo anti deppression,insomnia da kuma stress.

Za a hada shayin diyan kurna sai a sha rabin cup kamin a kwanta bacci inshaAllahu za a samu natsuwa kuma jiki zai samu hutu a daren.zaka tashi a cikin karfin jiki ba kasala ba damuwa ko ciwon jiki.

 

3.Kurna na maganin cutukkan ciki wadanda suka hada da majinar ciki (intestinal mucus),da kumburin ciki da ciwon ciki da tsuwar ciki da zafin ciki da rashin iya cin abinci da sauransu wani nazari da aka wallafa a kasidar nan mai suna Journal of Agricultural and food chemistry ta bayyana cewa kwankwadar shayin kurna na adadin da ya kai na milligrams 40 a kowane wuni na rage mafiyawan cutukan da cike ke fama dasu da kuma wanke duk wani abu da zai iya illata ciki.(harmful compounds).

 

Karanta: Zaben Gwamnoni: Kar Ku Yi Sak, Ku Zabi Ra’ayin Ku – Inji Buhari

 

4.kurna na magance cutukkan babbar hanzanya da kuma sanya laushin bayan gari mai taurin da ya koma tamkar duwatsu a sabili da wasu matsaloli.
Wannan magani ne ingantacce.

 

5.Rikicewar jiki,kasala da yawan bacci da kuma ciwon jiki da ga6o6in jiki.
Sai a nemi ganyen kurna danye a dake sai a sanya ruwan dumi a tace da kyau a sha rabin cup da safe bayan an dawo wajen motsa jiki.

 

7.Masu rashin lafiyar ta6in hankali suma zasu amfana da ganyen kurna.Dan karin bayani kan wannan matsalar sai anememu a inbox.Ba kowane magani doka ta bada umurnin bayarwa ba.

 

Karanta: Amfanin Tsamiya Da Kuma Ilolinsa Ga Lafiyar Dan Adam

 

8.Wanda ke da karamcin sinadirran Vitamin C ko mai yawan fama da rashin lafiya ko wanda ciwo ke jimawa a jikinsa bai warke ba. Sabili da low immunity sai ya rinka hada ruwan zafi na diyan kurna yana sha.Ko baya ga wannan zai samarda kyan fatar jiki da magance kurajen fata dama wadanda ke fitowa ga harshe ko a cikin baki (oral thrush,skin diseases)

 

9.Hauhawan jini- yawan sinadiran potassium dake kumshe da kurna ya bata damar safkarda hauhawan jini.

 

10.Matan da suka haihu zasu iya amfani da ganyen kurna su tafasa sai su rinka wanka da ruwan dumin dan samun karfin kassan jiki da ma inganta lafiya da kashe wasu kwayoyin cuta ko rage kumburin kafafu kona jiki bayan haihuwa.

 

Karanta: Abubuwa 4 Da Suka Sanya Fadiwar Atiku A Zaben Shugaban Kasa

 

10.mai fama da tsohuwar shawara (jaundice) ko lailayin wani ciwo a jiki da ya rasa gane kansa sai ya nika busashen ganyen kurna sai ya koma gari sai ya rinka sanya dan karamin cokali daya a cikin nono marar tsami yana sha.

 

Wanda aka sara da karfe wuka ko takobi ko adda shi ma zai iya amfani da sayyun kurna da kuma Cumin sai a tafasa a diga zuma kadan sai a rinka sha za a warke nan take da amincin Allah.

Mai neman shawara ko tambaya ko korafi ko wata matsala ko wani taimakon da zamu iya kofa a bude take.
Wallahi tallahi ba cuta ba karya ba yaudara da fatar Allah ya mana jagora.
Alhamdulillah.

Leave A Reply

Your email address will not be published.