GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Maganin Radadi Da Zafin Ciwon Hakori

Maganin Radadi Da Zafin Ciwon Hakori

174

- Advertisement -

Ciwon hakori ciwo ne mai zuwa da dan karen radadin zafi wanda har ya kan janyo ciwon kai. Ga  wasu hanyoyi mafi sauke wajen magance radadin ciwon hakori.

 

Karanta: Cututtukan Da Tafasasshen Ruwan Albasa Ke Magancewa

 

Kayayyakin Da Ake Bukata

– Ruwa

– Gishiri

– Ganye Gwaiba (Guava)

– Kofi

 

Yadda Ake Hadawa

 

A farko da za a tafasa ruwan sannan sai a zuba ruwan cikin kofi, daga nan sai a zuwa gishiri cokali 1 na cokalin shayi (wato teaspoon) sai a juya gishirin har sai a bace a cikin ruwan, sannan sai a dauke ganyen gwaiba kwara 2 a saka cikin kofin.

 

Karanta: Amfanin Tsamiya Da Kuma Ilolinsa Ga Lafiyar Dan Adam

 

Yadda Ake Amfani Da Maganin

 

Bayan an hada maganin sai a dauka kofin a kuskure baki da shi har sai ruwa ya taba hakorin  da ke ciwo, a yi hakan akalla sau 3 a rana, da yardan Allah za a samu sauki lamari.

 

Karanta: Maganin Harbin Kunama

 

Abun Kulawa

Abun kulawa a nan shine za’a yi amfani kofi 1 wajen kuskure bakin a kowane lokaci har sau 3 a rana wato da safe, rana da dare.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.