GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Shugabannin Hukumar NBS

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Nadin Shugabannin Hukumar NBS

29

- Advertisement -

Majalisar dattawa ta amince da nadin mukaman shugaba Muhammadu Buhari a hukumar kididdiga ta kasa.

 

Karanta: Kotu Ta Tabbatar Da Hon. Abdullahi A Matsayin Dan Takarar Majalisar Wakilai Na APC

 

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Majalisar ta amince da kudirin shugaba Buhari, biyo bayan samun rahoton sakamakon binciken da kwamitin tsare-tsaren kasa da kuma tattalin arziki na majalisar ya gabatar.

 

Majalisar dai ta amince da Kabiru Nakaura a matsayin shugaban hukumar kididdiga ta kasa mai reshen Arewa maso Yamma.

 

Karanta: Matakan Tsaro: Ku Gudanar Da Aiki Yadda Ya Kamata, Ba Sani Ba Sabo – Inji Buhari

 

Sauran shugabannin hukumar kuma sun hada da Akinola Bashir daga Kudu maso Yamma, da Moses Momoh daga Kudu maso Kudu, da Wallijoh Ahijoh daga Arewa ta Tsakiya, da Adam Modu daga Arewa maso Gabas, da kuma Nwafor Chukwudi daga Kudu maso Gabas.

 

Karanta: Hadiza Gabon: Tsakanin Zargi da Gaskiya

 

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, ya taya sabbin shugabannin murna, tare da yi masu fatan alheri, ya na mai gargadin su a kan jajircewa wajen yi wa kasar su hidima.

Leave A Reply

Your email address will not be published.