GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ware Naira Biliyan 10 Ga Zamfara

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ware Naira Biliyan 10 Ga Zamfara

21

- Advertisement -

 

Majalisar Dattawan ƙasar nan ta tsayar da ƙudirin ware Naira biliyan 10 daga kasafin kudin 2019 domin kula da mutanen da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a jihar Zamfara.

 

Karanta: Dandazon Ƙudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Hukumar Kwastan

 

Majalisar ta dauki matakin ne bayan muhawarar da Sanata Kabiru Garba Marafa na jam’iyyar APC daga jihar Zamfara ya gabatar a ranar Laraba.

 

Marafa ya bukaci samar da kudaden tallafi domin agazawa mutanen da rikicin jihar Zamfara ya raba da muhallansu ko kuma ya shafa.

 

Karanta: Sojoji Sun Ƙwace Mulki Daga Hannun Omar Hassan Al-bashir Na Sudan

 

Majalisar ta yi Allah-Wadai da kashe-kashen da ake fama da su a jihar, in da ta jinjinawa al’ummar ƙasar nan akan yadda suka yi fitar-dango domin nuna goyon bayansu ga al’ummar jihar.

 

Kazalika Majalisar ta koka kan yadda matsalar tsaro ta tabarbare a wasu sassan ƙasar nan da suka hada da Kaduna da Katsina da Sokoto da Filato da Benue da Taraba da sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.