GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Makulashe: Yadda Ake Hada Samosa Mai Dan Karan Dadi

Makulashe: Yadda Ake Hada Samosa Mai Dan Karan Dadi

204

- Advertisement -

Kayan hadi:-

•Filawa

•Butter

•Gishiri

•Mai

•Nikakken nama ko kifi

•Albasa

•Koran tattasai

•White pepper

•Thyme

•Curry

 

Karanta: Mata, ku kiyayi kwana da dan kamfai – wani kwararre

 

YADDA AKE HADAWA

 

Kwaba filawa da mai ko butter,gishiri da ruwa kamar na meat pie. rufe ajiye har zuwa minti 20. raba filawa gida 4.

 

Murza vari daya kan katakwan yanke yanke (Chopping board) har sai tayi lafai-lafai. kada yayi kauri sai a shafa man gyada akai da burushi irin na masu fenti dan karami (Pastry brush).

 

Sake dauko wani varin na filawa murza shi kamar yadda aka yiwa na farko.dura shi saman wancan da kika shafawa mai kuma murzawa.itama shafa mata mai.haka za ki tayi har agama gaba daya (ana shafa mai dan kada su manne da jikin su). idan anzo na karshe sai asa filawa.

 

Karanta: Yadda ake Amfani Da Madara Wajen Magance Maikon Fuska

 

Shafa mai a cikin tire irin wanda ake dora cake aciki. dauki kwabin a hankali daura kan tiren. kunna oven ki matsa kaicin zafi (moderate) har zuwa minti 20. Ko kuma idan anga ya fara dagowa yana rabuwa da junansa. fito dashi sai a yanka gida biyu dai dai.

 

Sai a nadeshi kamar kwakkwaro zuba nama aciki rufe bakin da filawa da’aka kwaba da ruwa. soya cikin mai mai zafi. yadda ake soya naman cikin samosa.

 

Karanta: Cututtukan Da Tafasasshen Ruwan Albasa Ke Magancewa

 

Zuba niqaqqen naman a kasko da Maggi/Gishiri, tafarnuwa, w/pepper da mai kadan idan naman ya soyu zuba albasa da koran tattasai sauke

Leave A Reply

Your email address will not be published.