GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Makulashen Sallah: YADDA AKE DANBUN NAMAN KAZA

Makulashen Sallah: YADDA AKE DANBUN NAMAN KAZA

401

- Advertisement -

Idan kika gyara kajinki tas! Saikicire masa fatar dake jiki gaba dayakiwanke yadda ya kamata Saiki zubaa tukunya amma kizuba ruwa kwatankwacin yadda naman zai shanye,

 

Karanta: HANYOYIN KARIYA DAGA HADURRAN ABIN HAWA

 

Kar ki zuba dayawa, ki dora kiyanka albasa, maggi, gishiri, curry, da kayan kamshi zabin ki, sai ki rufe kibar ta tayi tafasa dakin bude kin ga naman yayi laushi zaki sauke Kasa sa iki sa muciya kiyi ta faffasa naman idan baki cire fatar yana danye ba,

 

Karanta: Hanyoyin Kariya Daga Saran Maciji

Toh, yanzu sai ki zare duk fatar da manyan qashi kiyta faffasawa zakiga naman yafito sanka-sanka saiki jajjaga taruhunki sosai.

 

Ki juye akai ki qara curry da kayan qamshin dakike so, ki gauraye ya hade naman, sai ki samu abun suya mai dan dama kizuba mai dayawa cux inkika masa qwauron mai kwata kwata ba zai yi kyau ba.

 

Karanta: HANYOYIN KARIYA DAGA CUTAR KANJAMAU

 

Sannan bazai laushi ba,saiki dauko namanki kijuye aciki kidora awuta kipara soyawa sannan kisa wuta kadan ahankali kina juyawa akai akai,idan ya soyu zakiga yayi ja sannan mai
zai kara kumfa kuma zakiji kamshi sai ki sauke kijuye a colander ya huce sai ki dan saka plate asama kimatse mai duk zai fito, shikenan!

Leave A Reply

Your email address will not be published.