GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Makulashen Shan Ruwa: Yadda Ake Girka Farfesun Kifi Mai Dan Karen Dadi

Makulashen Shan Ruwa: Yadda Ake Girka Farfesun Kifi Mai Dan Karen Dadi

380

- Advertisement -

FARFESUN KIFI

ABUBUWA DA AKE BUKATA

kifi
Citta
Taruhu
Kanin fari
Curry
Thyme
Albasa
Maggi
Tafarnuwa
Gishiri
Daddawa inkina so

 

Karanta: Menene Tushen Jin Dadin Aure?_ JIMA’I (Ku Karanta)

Da farko zaki wanke danyen kifinki da lemon tsami don ya rage qarni ki wanke kifin sosai, saiki jerashi yasha iska, sannan zaki dauko taruhun ki ki jajjaga shi, saiki daka citta kanimfari ya zama gari, sannan in zakisa daddawa ita ma ki dakata ta zama gari,

 

in bakya buqata shikenan, zaki yanka albasan ki yanka manya manya, sannan saiki dora ruwa daidai yadda bazai rufe kifin ba a tukunya ya tafasa, zaki kawo kayan miyanki taruhu, daddawa, kanimfarin citta, maggi gishiri ki juye a ruwan yayi ta tafasa sai warin daddawan ya fita saiki kawo kifin ki kijera a tukunyan, ki kawo albasan ki kijuye da curry da thyme,

 

Karanta: HANYOYIN KARIYA DAGA ZAZZABIN LASSA FEVER

 

ki dan gurza tafarnuwa kadan, sai ki rufe tukunyan ki lura kifi bashida wahalan dahuwa in ya dahu da yawa zai farfashe, aci dadi lafiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.