GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Malami Ya Sa An Kona Dalibarsa

Malami Ya Sa An Kona Dalibarsa

37

- Advertisement -

A kasar Bangladesh, wata daliba ta yi gamo da azal na rayuwa, inda aka kone ta kurmus bisa ummurnin shugaban makaranta bayan ta tona masa asiri na laifin keta mata haddi kamar yadda hukumar ‘yan sandan kasar ta bayyana a ranar Juma’a.

 

Karanta: Kwankwaso Jahili Ne Ko Sharar Masallaci Bai Chanchanta Ya Samu Ba Bare Shugaban Ƙasa – Inji Dr Isah Ali Pantami


Mutuwar wannan budurwa mai shekaru 19 kacal a duniya, Nusrat Jahan Rafi, ya haifar da mummunar zanga-zanga a yankin kasar dake nahiyyar Kudancin Asia. Firai Ministan kasar, Sheikh Hasina ya sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin wannan zalunci.


Bayan da masu hannu cikin wannan muguwar aika-aika sun gaza samun biyan bukata yayin da suka nemi Nusrat ta janye korafin keta mata haddi, sun yi mata wanka da makamashi na Kalanzir kuma suka kone kurmus.

 

Karanta: Na Yi Wa Sarki Sanusi Nisa, Shugaban Ƙaramar Hukuma Ne Dai-Dai Da Shi – Inji Gwamna Ganduje


Hukumar ‘yan sanda yayin karin haske dangane da wannan lamari na takaici ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke mutane 17 ababen zargi inda daya daga cikin su ya amsa laifi sa da cewa sun aikata hakan ne bisa umurni na shugaban makaranta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.