GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Mata Masu Buri Sun fi Rashin Miji Da Shan Wahalar Aure

Mata Masu Buri Sun fi Rashin Miji Da Shan Wahalar Aure

316

- Advertisement -

Duk rashin mijin da ake yi a arewacin Najeriya bai hana yawan bukukuwan da ake yi ba saboda a daidai lokacin da wasu suke kuka wasu kuma dariya suke yi.

 

Duk irin fatarar miji da ake yi, mata masu kamun kai da saukin rayuwa suna samu, kusan duk karshen sati sai an aurar da mata da yawa, babu shakka akan hakan.

 

Karanta: Wata Kungiya Ta Nemi Sanata Goje Ya Yi Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa Ko Ta Kai Shi Kotu

 

Amma saidai akwai da yawa daga cikin ‘yan mata a zaune suna ta jiran miji. Wasu salihai ne, kawai jarraba ce daga Allah, wasu kuma halayyarsu ce ta jawo musu. Kamar yadda Allah yace, idan kaga da kyau daga nine, sa6aninn haka kuwa daga bawa ne tunda ba zai yiwu ba Allah ya umarci bawa da sa6onsa kuma daga baya ya hukuntashi.

 

Ba zai yiwu ba a samu bayin Allah suna zuwa wajenki kina korarsu saboda basu da kudi kuma kice kina cikin jarrabawar Allah, Ta ina? Mata da yawa a cikin al’umma suna daukar rayuwar aure kamar a wasan hausa. Misali, a wasan hausa ne ake nuna miji da mata a qaton gida da manyan motoci a cikin rumfa, ga kuma ‘yan aiki a gidan sai abunda ake so za a ci.

 

 

Hakan ne yasa ko sun yi auren suke rayuwa cikin kuncin zuciya saboda sun dauko dala ba gammo. Tabbas masu rabo suna samun hakan a rayuwa amma basu da yawa daga cikin al’umma, kada ki yaudari kanki ‘yar uwa, kowa da irin rabonsa a rayuwa, idan Allah yaso sai ki samu irin wanda kike so, idan kuma bai qaddara miki haka ba sai gidanku yafi gidan mijinki arziki koda babanki attajirin gaske ne.

 

Karanta: ‘Yan Sanda Sun Kama Yaran ‘Yan Shi’a 43 A Kaduna

 

Kowa da kaddararsa. Ke kuma ‘yar talaka ahirrrr dinki, kada ki biye wa ‘yar me kudi ko qawa, ki yi addu’a Allah ya baki miji nagari tunda dama bi ki tashi a cikin kudi ba ballanta ayi miki uzuri don an sameki da buri. Zai wahala a samu mace wacce bata ta6a samun damar aure ba a rayuwarta. Misali, wani bai ta6a cewa yana sonta da aure ba tunda take.

 

Gaskiya da kamar wuya gurguwa da auren nesa, wata ma zaka samu labarin samari sun zo da yawa amma ta raina arzikinsu kuma ta dawo tana neman qasa da su. Har a cikin ‘ya’yan masu kudi ma zaka samu mace ta kai shekara arba’in babu miji kuma lafiyarta kalau.

 

Gaskiya dole ba zaki samu ba saboda kin sha ruwan alkausara kin ce sai wanda yake da gidan da yafi na babanki ko kuma wanda yafi mijin yar uwarki ko qawarki arziki. Babu shakka wannan dalilin ne yasa maza suka koma auren jari, mata suna neman miji mai kudi su kuma sana neman auren ‘yar maikudi wacce babanta zai basu kudi.

 

Karanta: An Kama Mutanen Da Suka Yi Zargin Bacewar Shanunsu 31 A Ofishinan ‘Yan Sanda

 

Shiyasa ake shan wuya kwarai da gaske, shi babu mata, ke kuma babu miji. Musamman yanzu da kudi suke wahalar samu, duk macen da take neman miji mai kudi to saidai ta auri mai mata biyu ko uku don shine ya dade yana neman kudi ko aiki. Mu ajje buri don mu samu sassauti a rayuwar nan. Insha Allah, Allah zai bawa kowa abunda yake so na alheri. Allah ya shiryar damu.

 

Daga Comrade M.K Soron Dinki

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.