GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Mata Masu Zaman Kansu A Abuja Sun Zargi ‘Yan sanda Da Yi Musu Fyade

Mata Masu Zaman Kansu A Abuja Sun Zargi ‘Yan sanda Da Yi Musu Fyade

28

- Advertisement -

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil mata sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kamen da hukumar kare muhalli ta Abuja ta yiwa wasu mata masu rawa tsirara a wani gidan rawa da ke Jabi a Abuja.

 

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Wargaza Garuruwa Sama Da 98 A Jihar Zamfara

 

Wasu daga matan wanda yawansu ya wuce sittin sun yi zargin jami’ai sun ci zarafinsu, inda har su ka ce ‘yan sanda sun yi mu su fyade a caji ofis.

Matan daya bayan daya da suka hada da shugabar mata masu zaman kansu ta Nijeriya Amaka Naara sun gabatar da kansu da korafin an kama su ba bisa ka’ida ba.

Karanta: Da Dumi-Dumi: ‘Yan Sanda Sun Gano Makamai A Ofishin Jam’iyyun PDP Da APC Ta Jahar Kano

Daya a cikin mata masu zanga-zangar mai suna Amaka ta ce “a kullum ‘yan sanda na kawo mana samame a otal-otal da mata masu zaman kansu ko tarawa da maza a biya awalaja, su kan karbi kayyadedden kudi na goro a wajen mu don barin mu, mu yi sana’a.”

“Abin da ya ban mamaki shi ne jami’an sun caje mu da yawon banza, ni ban gane yadda hakan ya ke da ma’ana ko alaka da lamarin tara kudin shiga ba.

Ta kara da cewa a Lagos akwai ‘yan sanda da su kan biya kudi don a kyale su, kuma da zarar an yi sabon DPO sai a zo a damke su sai sun biya kudi ko kuma wani lokacin ‘yan sandan na neman kwanciya da matan kyauta ne.

 

Karanta: An Yi Aure Babu Amarya Saboda Ango Ya Kasa Samun Mata

 

Matan sun ce ‘yan sandan kan kama su su karbi kudi daga bisani su dawo su neme su, suna masu al’ajabin in har za a kama su mata me ya sa ba za a damke maza masu neman su ba.

Sun yi zargin bayan an tattara su, wasu da suka kasa belin kansu, sun fada tarkon jami’an da suka yi mu su fyade ba da kwaroron roba ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.