GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Matsafa Sun Yiwa Wasu Kananan Yara Yankar Gunduwa-gunduwa

Matsafa Sun Yiwa Wasu Kananan Yara Yankar Gunduwa-gunduwa

121

- Advertisement -

 

Hukumomi a Tanzania sun ce an kashe yara shida a kudu maso yammacin kasar sannan aka cire kunnuwa da hakoransu.

Kazalika an gano cewa an cire yatsun yaran, wadanda shekarunsu suka kama da shida zuwa tara.

 

Karanta: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i (Shawara Ga Maza)

 

Kwamishiniyar lardin Njombe Ruth Msafiri ta ce “An yi hakan ne domin yin tsafi da sassan jikin nasu kuma wasu na ganin za su zama attajirai idan suka yi tsafi da sassan jiki.”

‘Yan sandan sun tsare wani mutumwanda dan uwa ne ga uku daga cikin yaran, bisa zargi da hannu a kisan su.

 

Karanta: Wata Mata Ta Kashe Mahaifiyarta Ta Hanyar Sassaranta Da Adda

 

Yara goma ne suka bata a lardin Njombe tun farkon watan Disamba ko da yake an gano hudu da ransu.
Wasu Yanjarida sun ce matsafa ne suke sanya wa a kashe yara sannan aka cire wasu sassan jikinsu domin yin asirin da wasu ke gani zai sa su zama attajirai.

 

Kwamishiniyar ta shaida wa majiyar mu cewa “Muna kira ga iyaye da su sanya ido sosai kan yaransu sannan su rika gaya musu inda za su idan sun fita.”

 

Karanta: Mahaifiyar Mu Ta Ban Guba Na Saka Cikin Abinci Da Ruwa Wankar Mahaifin Mu – Da Ya Fadawa Kotu

 

An sace yaran ne daga gidajensu da tsakar dare lokacin iyayensu sun tafi kasuwa inda suke kasuwanci.

Allah Sarki. Dama dai suna koyawa yaran adduar fita daga gida wacce Annabi S.A.W ya koyar domin kare afkuwar hakan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.