GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Mayakan Boko Haram Sun Kwashi Kashinsu A Hannu A Wata Gwabzawa Da Suka Yi Da Sojoji

Mayakan Boko Haram Sun Kwashi Kashinsu A Hannu A Wata Gwabzawa Da Suka Yi Da Sojoji

29

- Advertisement -

Rundunar Sojin Najeriya ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe mata sojoji guda 5, lokacin da suka kai hari sansaninsu da ke Magumeri a Jihar Borno.

 

Karanta: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

Mai Magana da yawun sojin, Ezindu Idima ya bayyana cewar bayan kazamin harin da mayakan suka kai, anyi artabu sosai da maharan, wadanda suka afkawa sansanin sojin da yawa domin satar abinci, abinda ya baiwa sojin damar dakile harin.

Kakakin sojin yace dakarunsu sun yi nasarar jikkata maharan da dama, yayin da suma suka rasa sojojinsu guda 5.

Rundunar sojin Najeriya, ta fitar da wannan sanarwar ce, bayan da a jiya Lahadi, tsagin mayakan kungiyar ta Boko Haram da ke yi wa kungiyar IS biyayya, yayi ikirarin hallaka dakarun kasar 10, a farmakin da suka kaiwa sansaninsu da ke garin Magumeri da ke jihar Borno.

 

Karanta: RAMADAN: Boyayyun Hukunce Hukunce Game Da Azumi

 

Majiyar tsaro ta ce, mayakan haye akan babura da manyan motoci sun far wa sansanin sojin da ke Magumeri mai tazarar kilomita 50 daga birnin Maiduguri da yammacin wannan Jumma’ar da ta gabata.

Mayakan sun shafe tsawon sa’o’i 4 suna cin karensu babu babbaka a sansanin, in da suka kwashe makamai kafin daga bisani a yi nasarar fatattakar su, da taimakon barin wutar dakarun sojin saman Najeriya da karin wasu sojin na kasa da aka tura zuwa garin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.