GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Mutane 1500 Za Su Amfana Shirin Gwaji Da Bada Maganin Asibiti Kyauta Na Hon. Abdullahi I. Garba (Bidiyo)

Mutane 1500 Za Su Amfana Shirin Gwaji Da Bada Maganin Asibiti Kyauta Na Hon. Abdullahi I. Garba (Bidiyo)

87

- Advertisement -

Akalla mutane 1500 da ke karkashin mazabar Kontagora/Wushishu/Mariga/Mashegu majalisar tarayya za su amfana da shirin bada magani da gwajin kiwon lafiya kyauta a jihar Neja.

 

Karanta: Amfanin Aya 7 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilai na tarayya, Hon. Abdullahi Idris Garba (wanda aka fi sani da Mai Solar) ya shirya wannan shirin na kwanaki 5 don habbaka harkar kiwon lafiya a mazabarsa. A cikin shirin likitoci za su bada magunguna kyauta, maganin sauro.

 

A shirin za a yi gwajin kwayar cutar kanjamau tare da fadakarwa a kan cutar, za a gwada shugan mutane, da zazzabin cizon sauro, da ciwon hakori da makammancinsu.

 

Wata matan aure wacce ake kira da suna, Amina Isah, tana daya daga cikin mutanen da suka amfana da wannan shirin ta yi mika godiyarta na musamman a kan shirin da aka shiryawa al’umma musamman ma gwajin hawan jini da ciwon shuga da ake yi kyauta.

 

 

Ta ce, “Bana jin dadin jiki na sannan kuma ina tsoro zuwa asibiti a gwada ni saboda sannin nawa zan kashe wajen yin irin wadannan gwajin. Mutane da dama kamar makwabta na sun dade suna fama da cututtuka da dama amma ba su da damar zuwa asibiti domin a gwada su saboda ba su da isasshen kudi.

 

Karanta: Kadan Daga Cikin Ilolin Tsaka

 

“Na yi matukar jin dadi da aka kawo mana wannan shirin a yankin mu. Musamman a irin wannan lokaci da kasar ke fama da kariyar tattalin arziki, mafi yawancin mu ba mu iya zuwa asibiti domin a yi mana gwaji. Amma ya kawo mana likitoci domin su gwada mu sannan kuma su ba mu magani kyauta. Ina fatan sauran ‘yan majalisa masu wakiltar mu za su yi koyi da hakan.”

 

Wani bawan Allah da shi ma ya amfan da wannan shirin, Ibrahim Tanko, ya yiwa dan majalisar da tawagar likitocin da suka zu gwada su godiya ta musamman a kan irin kulawa da suka baiwa mutane.

 

Karanta: Amfanin Ganyen Mangwaro 7 Ga Lafiyar Dan Adam

 

 

“Tun a farkon wannan shekarar, na fara  fama da rashin isashen kudin siyar magungunan asibiti hadda ba rashin kudi yin gwajin asibiti. Amma a yau, an ba ni magani kyauta, da maganin sauro, har yanzu ina mamakin wai wannan abun kyauta ne. Har yanzu ba yadda hakan gaskiya ba ne.”

 

 

A farko da, a yayin da manema labarai suka yi magana da wanda ya kaddamar da wannan shirin, Hon. Abdullahi Idris Garba (MAI SOLAR) a wayar tarho ya e, ya hakan na daya daga cikin kudirinsa na gyara harkar lafiya a mazabarsa tare da tallafawa marasa isashen kudi wajen samar masu magunguna don magance cututtukan da suke fama da shi.

 

 

Ya fadawa yanar gizon GULMAWUYA ce ya kaddamar da shirin domin ya gyara habbaka harkar kiwon lafiya a mazabarsa tare da tallafawa talakawa marasa isashen kudin magunguna samar da magungunan da ya kamata domin kula da lafiyarsu

 

Ku kalli bidiyo da hotuna a kasa;

ho

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.