GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina - Buhari

14

- Advertisement -

Bayan saukarsa daga jirgi daga ziyarar da hukumomi a fadar shugaban kasa suka bayyana da ziyarar ƙashin kai, Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da manema labarai, inda ya amsa tambayoyi da dama.

 

Karanta: RAMADAN: Addu’ar Yin Bude Baki

 

Wani daga cikin manema labaran ya tambayi shugaba Buhari cewa: “Wadanne irin mutane za mu yi tsammani a majalisar zartarwarka a wannan karon?”

 

Buhari ya amsa tambayar da cewa, tabbas ya kammala shirye-shiryen nau’in mutanen da zai zuba a sabon majalisar zartarwarsa don cimma muradan mataki na gaba. Amma sai ya kara da cewa amma ba zan fada maka ko su wane ne mutanen ba.

 

Karanta: RAMADAN: Boyayyun Hukunce Hukunce Game Da Azumi

 

“Amma tabbas yanzu na shirya tsaf don na gabatarsu ga al’ummar Nijeriya sannan kuma na rantsar da su a matsayin ministocina,” inji Buhari.

Leave A Reply

Your email address will not be published.