GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Na Yi Nadamar Shan Kwatami Domin Murnar Zarcewar Buhari – Inji Ali Gayu

Na Yi Nadamar Shan Kwatami Domin Murnar Zarcewar Buhari - Inji Ali Gayu

102

- Advertisement -

Matashin nan da ya tari aradu da ka, ya sha ruwan kwatami gami da yin birgima da shi, saboda murnar zarcewar Shugaban ƙasa Muhammad Buhari a karo na biyu, wato Ali Gayu, ya nuna nadamarsa akan yadda a ka yi wofi da shi duk da ya sadaukar da lafiyarsa da rayuwarsa, don ya burge masoyan Buhari.

Karanta: Kisan Zamfara: Zamfarawa Ba Sa Kwana A Gidajen Su Yanzu- Marafa

Idan za’a iya tunawa dai, daf da bayyana cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu nasara a zangonsa na biyu, wani matashi mai suna Ali Muhammad Sani ya fada cikin kwata da shan ruwanta duk dai domin murna da zarcewar Buhari, kana matashin ya yi suna a ciki da wajen kasar nan domin an yada cewar a sakamakon shan kwatamin ya ma mutu.

Ali Gayu ya nuna wannan takaicin nasa ne a zantawarsa da manema labarai, inda ya bayyana cewar ya kasance matashin da ya tari aradu da ka wajen sallama wa lafiyarsa da lokacinsa don shan kwata dukka domin murnar nasarar Buhari.

Matashin mai shekaru 23 a duniya ya ƙara da cewa, da gwamnatin Buhari tana damuwa da masoyanta da ta jawo shi a jika tare da yi masa goma ta arziki, amma ya ce har zuwa yanzu shiru kake ji kamar an shuka dusa.

“Ka san dai ni ne mai suna Muhammad Aliyu Sani wanda aka fi sani da Ali Gayu, daga unguwar Doya a cikin garin Bauchi, ni ne wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce a kaina a lokacin da na sha kwata domin murna da zarcewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

“Na sha suka da zagi da yabo a lokacin da na sha kwatami da yin burgima a cikin kwatamin nan, na kau da kaina domin soyayyar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ban damu da matsalar da ta za ta biyu bayan abun da na yi ba”

“Babban abin da ke akwai ma shi ne na saida raina da lafiyata. A lokacin da aka yi ta cewa na mutu-na-mutu a sakamakon soyayyar Muhammadu Buhari, na sha kwata wanda kowa ya san kwata najasa ne wanda cuta ka iya kamani, amma cikin ikon Allah babu abun da ya sameni zuwa ga wannan lokacin,”

Ya ƙara da cewa abin da ya ba shi mamaki kuma ya dameshi shi ne har zuwa yanzu wannan gwamnatin da na yi wannan babban aikin domin ita kamar ba ta san yanayin abun da na yi ba, ko ba wanda ya damu da lafiyata domin babu wanda ya tuntubeni ya ji ko ya koshin lafiyata yake ba.

“Wannan abun da muka yi, yau da mun samu wani alheri na tabbatar wasu ma za su mora daga garemu domin akwai matasa sosai wadanda suke zaune basu da aiyukan yi, da ya dace mu a fanninmu mu taimaka musu ba ma sai an je ga wani fanni ba,”

Karanta: Facebook Na Shirin Fito Fa Hanyar Da Mutane Za Su Gane Masu Sonsu A Boye

A ƙarshe Ali Gayu Ya ce, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen kasar nan suka tuntubeshi akan wannan ɗanyen aikin da ya yi a wancan lokacin, yana mai shaida musu cewar har zuwa yanzu bai ga ribar aikin da ya yi ba tukun; domin haka ne yake mai kokawa akan gwamnatin shugaba Buhari da ta dubi wadanda suka mata hidima da idon basira domin kyautata rayuwarsu da lafiyarsu a kowani lokaci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.