GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Nau’ikan Abinci Da Ke Kashe Karfin Mazakuta (Ga Mazan Aure)

Nau'ikan Abinci Da Ke Kashe Karfin Mazakuta (Ga Mazan Aure)

113

- Advertisement -

1. Abincin Da Aka Sarrafa.

Abin nufi anan shine ire-iren abincin da ake sarrafawa a kanfuna a zuba su a mazubi dabam-dabam kamar leda, kwali buhu da sauran su.

Yayinda ake sarrafa wadannan nau’in abinci ana matukar rage masa sanadaran da ke da alfanu ga jikin mutum, wannan kuwa ya hada da sanadaran da ke ingiza sha’awa da kuma kara kuzarin namiji, da kuma wadanda ke karawa mace sha’awa da ni’ima.

Karanta: Ci Gaban Kasa: Ayyuka 19 Da Buhari Ya Bada Umarnin A Fara Yi Da Gaggawa

Binciken da masana suka gudanar akan alkama ya nuna cewa idan aka sarrafa ta zuwa filawa, to an yi hasarar wani sanadari na “zinc” da take kunshe da shi da misalin kashi uku bisa hudu. Wannan na nuna cewa idan ba’a sarrafa ta da na’ura ba ta fi amfani a jikin dan-adam.

Hakan na nuni da cewa yawaita amfanin da irin wannan nau’i na abinci lalle zai iya tasiri game da kuzari da sha’awar amarya da ango.

2. Sukari

Shi sukari da dangogin abinci masu yawan zaki ba kawai suna rage karfin sha’awa ba ne kadai, a’a harma da rage karfin mazakutar namiji.

Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa yawan shan sukari na rage yawan sanadarin halitta na “testosterone” a jikin mutum shi kuma karancin wannan sanadarin kan shafi jima’in mutum kwarai da gaske.

Saboda wannan dalili ne yasa ake bada shawara ga ma’aurata su guji shan sukari da ya wuce kima.

3. Maiko

Yawaita cin abubuwa masu maiko kamar kitse na haifar da wani maiko na cikin jini wanda ya ke toshe hanyoyin jini, ita kuma gudanar jini na da kyakkyawar alaka matukar gaske da jima’i.

Karanta: Abunda Ya Sace-sacen Kamfen Mata Ke Dada Tasiri – Inji Wani Malamin Addini

 

4. Abincin Gwangwani.

Nau’in abincin da ake sarrafawa sannan a zuba shi a gwangwani na haifar da matsala ga ma’aurata ta fuskar sha’awa da gamsar da juna.

5. Kayan Sha Na Gwangwani.

Wadannan nau’inkan abinci na da kamanceceniya da sukari, sai dai inda su ka sha bambam shine, su wadannan an sarrafa su, sannan kuma aka sa musu sanadaran da za su hana su lalacewa, kamar dai kayan abinci da aka sarrafa aka sa cikin gwangwani.

6. Kayan Toye-toye.

Su wadanan sun hada da irin su cincin, fanke, alkubus, da dai sauran nau’ikan wannan abinci. Su wadannan nau’ikan abinci suna hana jikinmu samun damar ribanyar wasu sanadaran halitta da ke da matukar muhimmanci ga ma’aurata yayin jima’i “testosterone” da kuma “estrogen” da turanci.

Bincike ya nuna a duk lokacin da aka ce wadannan sanadaran halitta sun yi kasa, to ba shakka hakan kan shafi yanayin sha’awa da kuma gamsar da juna.

7. Tabar Wiwi.

Ita dai mun sani haramun ce a addininmu na musulunci, hakan dokar kasa bata yarda ai safara ko shanta ba, amma duk da haka wasu kan zuke ta ko a boye ne.

Karanta: Illar Ruwan Tsarkin Bayan Gida Idan Ya Taba Al’aura (Shawara Ga Mata)

Bincike da aka gudanar akan ta ya nuna cewa tabar wiwi na sanya sanadarin nan na “testosterone” da muka ambata yin kasa sosai har na tsawon awa 24. Tabdijan, to mai karatu ai ko ba’a fada ba kasan wannan taba lalle za ta nakasa mai shanta, nakasawa kuma mai barazana ga dankon soyayyar aure harma da haihuwa.

Muna fatan ma’aurata za su nisanci wadannan nau’ikan abinci don samun ingantacciyar rayuwar aure mai cike da nishadi, kaunar juna da kuma zamantakewa abar kwatance. Allah Ya sa mu dace amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.