GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Radiance Beauty: Kwalliya A Lokacin Zafi

Radiance Beauty: Kwalliya A Lokacin Zafi

137

- Advertisement -

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.

 

Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:

 

Karanta: A Baiwa Duk Wanda Ya Ci Zaɓen Gwamna A Kano – In Ji Abdulmumin Jibrin Kofa

 

Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.

 

•Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.

 

Karanta: Yankin Arewa Na Da Buƙatar Jagororin Irin Sanata Kwankwaso – In Ji Sheikh Ibrahim Khalil

 

•Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.

 

•A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.

 

Karanta: Amfani Da Kuma Lahanin Cin Goro Ga Jikin Dan Adam

 

•Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.

Daga: Amina Abdullahi da Binta Aminu Saleh

Leave A Reply

Your email address will not be published.