GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Ramadan: Irin Kalar Abincin Da Ake So Mai Azumi Ya Rika Ci

Ramadan: Irin Kalar Abincin Da Ake So Mai Azumi Ya Rika Ci

55

- Advertisement -

Wani masani a harkar kiwon lafiyar dan Adam, Olu Aijota, ya bayyana ababen da suka dace mutum mai azumi ya rika ci a wannan wata mai tsarki.

 

Ga dai kadan daga ciki kamar yadda muka tsakuro daga shafin Premium Times;

 

Karanta wannan: RAMADAN: Addu’ar Yin Bude Baki

 

Yawaita Shan Ruwa

Yana da kyau a fara karya azumi da shan ruwa sai dai kuma ba a son a rika kwankwadar ruwa a lokaci guda wanda hakan yana iya sa ciki ya daure.

 

Karanta wannan: RIKICIN SARAUTA: Dan Majalisa Ya Maka Masarautar Gwandu A Kotu

 

Cin Ganye Da Abinci Mai Gina Jikin Dan Adam

Ya fi dacewa mai azumi ya nemi ganye ko kayan marmari yayin buda baki. Irin abin da ake nufi sun hada da kifi, lemu, gwaiba, abarba, ayaba, ganye da sauran su

 

A Guji Sukari

Dole mai azumi ya guji abubuwa irin su sukari da ice cream ko sinadarin soda. Irin wadannan sinadarai na kara nauyi don haka dole a guje su a cikin watan Ramadan.

 

Karanta wannan: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

A takaice dai ba a son cin abinci mai nauyi yayin azumi kuma ana bukatar a rika motsa jikin kafin ayi buda baki wannan zai kara lafiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.