GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

RAMADAN: Lokacin Da Yafi Daucewa A Yi Sahur

RAMADAN: Lokacin Da Yafi Daucewa A Yi Sahur

23

- Advertisement -

Tambaya ta 11 YAUSHE NE YAFI DACEWA AYI SAHUR?

.
Amsa. A sunnace anaso a Jinkirta yin sahur zuwa kusan ketowar Alfijir. Hadisi ya tabbata daga Anas dan Malik, daga Zaid bin Thabit (R.A.) yace “Mun ci Sahur tare da manzon Allah (S.A.W.) bayan wannan sai manzon Allah (S.A.W.) ya tashi zuwa sallah. Sai Anas ya tambayi Zaid bin Thabit minene tsakanin cin sahur da yin sallar Asuba?

 

Karanta: RAMADAN: Du’a for breaking fast

 

Sai ya ce gwargwadon Aya 50 (watau mutum ya karanta Aya 50)”. (Bukhari, 1921, muslim 1097). Akwai kuma hadisin Sahl ibn Saad yace:- “Na kasance ina yin sahur cikin iyalina bayan wannan sai in yi gaggawa domin samu Sujada (Sallah) da manzon Allah (S.A.W.)”. Wannan ya nuna cewa ana yin sahur ne dab da ketowar Alfijir (Bukhari, 1920).

 

Karanta: Ayyukar Ibadah Da Ake So A Yawaita Yin Su A Ramadan

 

 

.

Leave A Reply

Your email address will not be published.