GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Rashin Jima’i Akai-Akai Yakan Janyowa Mata Cutar Kwakwalwa – Masana

Rashin Jima'i Akai-Akai Yakan Janyowa Mata Cutar Kwakwalwa - Masana

92

- Advertisement -

Wata kwararrar likita a kan lafiyar kwakwalwa a kasar Nijeriya, Dakta Maymunah Kadiri, ta shawarci mata da su rinka saduwa da mazajen a kai a kai don rage yawan damu da kuma karin jindadin rayuwa.

 

Dakta Kadiri, wacce itace daraktan kiwon lafiya na asibitin Pinnacle Medical Service ta bada wannan shawaran ne a yayin da ake hira da ita inda ta ce jima’i bawai kawai gayar jikin mace kawai ya kai ba  yana taimawa lafiyar kwakwalwa mace.

 

Karanta wannan: An Cakawa Wata Mata Mai Dauke Da Juna Biyu Wuka A Wuya

 

“A matsayinmu na mata, yana da kyau mu mayar da mazajenmu kamar abokan mu idan har muna so mu samu cikakken lafiyar kwakwalwa. Bincike ya nuna cewa mata suna bukatan jima’i a kai a kai sannan a dangantakar aure tsakanin namiji da mata wadanda suka dade tare da juna, mata su kan shiga cikin damuwa musamman idan ba su samun jima’i kamar yadda ya kamata.

 

Karanta wannan: Wata Sabuwa: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Kananan Yara 2 A Zamfara

 

Saboda haka, jima’i na da matukar muhimmanci. Yana daya daga cikin abubuwan da ke magance matsalar yawan ciwon kai da mata ke fama da shi. Rashin isashen jima’i yana sanyawa mata yawan damuwa saboda ya kamata a yi duba ga wannan lamarin.

 

Mata su kan shiga cikin damuwa idan sha’awar jima’i ya fice masu. Yawan yawaita yin jima’i yana tamaikawa kwakwalwar ‘ya mace idan har tana son ta samu kyakyawar rayuwa,” inji Kadiri.

 

Karanta wannan: Kwastam Sun Kama Kwantenoni 12 Makare Da Kwayoyin Tramadol

 

Ta yi bayanin cewa ba wai anyi jima’i kawai don haihuwa bane kawai, inda ta kara da cewa jima’i na kara dankwon soyayya a tsakanin ma’aurata sannan kuma yana taimakawa wajen samun bacci mai kyau.

 

Dakta Kadiri ta yi kira ga mata wadanda ke fama da ciwon damuwa da su yawaita yin jima’i da mazajensu don magance wannan matsalar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.