GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Rep. Abdullahi Ya Horas Da Wasu Matasa Daga Cikin Jami’ansa Masu Kula Da Kafofin Sada Zumuntansa

Rep. Abdullahi Ya Horas Da Wasu Matasa Daga Cikin Jami'ansa Masu Kula Da Kafofin Sada Zumuntansa

197

- Advertisement -

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu a majalisar wakilai na kasa, Rep. Abdullahi Idris Garba (AIG) wanda aka fi sani da suna ‘MAI SOLAR’ ya horas da wasu matasa wadanda ke kula da kafofin sada zumuntansa wato Social Media Personnel.

 

Karanta: Yadda Ake Amfani Da Kwai Wajen Maganin Karfin Mazakuta

 

Wannan shine karo na farko a sanin mu a duk fadin kasar Najeriya da wani dan siyasa ke horas da wasu matasa wadanda ke kula da kafofin sada zumuntansa wato Social Media Personnel.

 

A yayin da mu ka yi hira da dan majalisan a wayar tarho ta salula dan majalisan ya “bayyana cewa yin hakan na da matukar muhimmanci domin kara wayar da wadannan matasan kai a kan yadda za su gudanar da ayyukansu da kyau ta hanyar wayar da kan al’ummar mazabarsa da kai game da ayyukar ci gaba da ya ke samarwa mazabarsa.”

 

Karanta: Hon. Abdullahi Shaidar Ya Karbi Takardar Shaidar Lashe Zabe, Yayi Alkawarin Ci Gaba Da Wakiltar Mazabarsa Yadda Ya Kamata

 

Dan majalisan ya kara da cewa “ya kamata a kai a kai a rinka wayar da kan matasa masu irin wannan aiki da kai domin aiki irin na su yana da matukar muhimmanci gama su irin wannan aiki musamman wajen wanzar da zaman lafiya ta hanyar sanin kalaman da za su furta wajen gudanar da aikinsu”

 

A karshe kuma dan majalisa ya ce “yayi kira da al’ummar mazabarsa da su ci gaba da zaman lafiya da junansu tare da daukar alkawarin ci gaba da yin iya kokarinsa wajen ganin cewa ya wakilce su yadda ya kamata a zauren majalisar tarayya da kuma ci gaba da samar yankinsa ci gaba”.

 

Karanta: Court confirms Hon. Abdullahi as APC’s house of rep. candidate

 

Wanda ya wakilci dan majalisar a filin taron, Shugaban yakin neman zaben dan majalisar, Alhaji Lawan Madangen, ya shawarci matasan da aka horas da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kara gyara ayyukansu.

 

Ga hotunan a kasa;

\

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.