GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Rikicin Mata: Uwa Da ‘Yarta Sun Watsawa Wata Ruwan Zafi Mai Dauke Da Yaji

Rikicin Mata: Uwa Da 'Yarta Sun Watsawa Wata Ruwan Zafi Mai Dauke Da Yaji

20

- Advertisement -

An gabatar da wata mata ‘yar shekaru, 50, Basirat Lamidi, tare da ‘yar ta ‘yar shekaru, 35, Taiye, a gaban wata kotun Majistare da ke Osogbo a kan zargin yunkurin kisa.

An caji matan 2 da laifin aikata laifuka 2 wadanda suka hada da makirci da yunkurin kisan kai.

Lauyar da ya mika karan zuwa kotu, Sifeto Gafari Musilimi, ya ce wadanda ake zargi sun yunkurin kashe wata mata, Rebecca Oladosu, ta hanyar wata mata ruwan zafi da yaji a jiki.

“Sakamakon ruwan zafin da suka zuba mata, matar ya samu rauni sosai a jikinta.

“Matar da aka watsawa ruwa zafin tana kwance a asibiti inda likitoci ke kokarin ceton ranta,” ya ce.

Lauyar da yta mika karan zuwa kotun ya ce wadanda ake zargi sun aikata laifin ne a 10 ga watan Oktoba a kauyen Okeyuka a jihar Osun.

A cewarsa, laifin ya sabawa sashe 516 da 320 na kundin dokar jihar Osun, 2003.

Su wadanda ake zargi, duk da haka sun karyata laifin da aka gurfanar da su a kai

Alkalin kotun, Mrs Falilat Sodamade, ta bada belin wadanda ake zargi a kan kudi naira N500,000 tare da kawo wakili 1 a kan kowane daga cikinsu.

Sodamade ta ce wakilan sai sun kasance masu zama a jihar sannan kuma sai sun kawo shaidar biyan haraji.

Ta daga saurarar karar zuwa 13 ga watan Nuwamba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.