GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

RIKICIN SARAUTA: Dan Majalisa Ya Maka Masarautar Gwandu A Kotu

RIKICIN SARAUTA: Dan Majalisa Ya Maka Masarautar Gwandu A Kotu

14

- Advertisement -

 

Zababben Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Koko Besse da Maiyama a majalisar wakilai ta kasa, Shehu Muhammad (Wambai) ya garzaya da masarautar Gwandu dake jihar Kebbi gaban kuliya inda yake zargin wasu jami’an masarautar ta Gwandu da hada kai da wasu jami’an masarautar garin Koko da nisanta zuri’arsa ga gadon sarautar garin Koko.

 

Karanta: Mayakan Boko Haram Sun Kwashi Kashinsu A Hannu A Wata Gwabzawa Da Suka Yi Da Sojoji

 

Shehu Muhammad na ganin ya gadi sarautar garin Koko amma an nisanta danginsa da gadon sarautar wanda hakan ya sa ya garzaya kotu domin kwatowa danginsa hakkinsu.

 

Ana dai shari’ar ne a babbar kotun tarayya dake birnin Kebbi, kuma tuni an yi zaman sauraren karar a ranar 25-04 na wannan shekara. Kuma mai shari’a ya saka ranar 18 ga wannan wata a matsayi ranar cigaba da sauraren karar.

 

To Saidai ba nan gizo ke saka ba, al’umma na cigaba da bayyana ra’ayinsu game da wannan shari’a inda wasu ke ganin wannan lamari tamkar cin fuska ne ga masarautar. Wanda ba a taba samun wani can gefe da ya maka masarautar gaban kotu ba.

 

Masarautar Koko dai tana karkashin masarautar Gwandu ne wadda ta na daya daga cikin manyan masarautun gargajiya a Nijeriya ba wai Arewa kawai ba, masarautar da ta samo asali daga Abdullahin Gwandu kani ga shehu Dan fodiyo.

 

 

Karanta: Na Kammala Tsara Kunshin Mutanen Da Za Su Kasance Ministocina – Buhari

 

Shehu Wambai tsohon jami’in Dan sanda ne da ya taba zama dogarin tsohon gwamnan jihar Katsina kafin ya ajiye aiki ya shiga siyasa.

 

Abun jira a gani shine yadda za ta kaya tsakanin masarautar da Shehu a zama na gaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.