GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Samar Da Aiki: Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Sake Gudunar Da Shirin Rabon Awaki

Samar Da Aiki: Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Sake Gudunar Da Shirin Rabon Awaki

21

- Advertisement -

Gwamnatin jihar Jigawa zata gudanar da rabon awaki kashi na biyu ga kananan hukumomin da suka cika sharuddan dawo da awakin da raba a kashin farko.

 

Karanta: Amfanin Ganyen Kuka Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Kwamishinan aikin gona da albarkar kasa Alhaji Kabiru Ali ya sanar da hakan a lokacin wani taro da kwamitin rabon awaki na jiha.

Yace gwamnatin jiha ta kammala duk wani shiri na rabon awakin kashi na biyu da nufin bunkasa tattalin arzikin matan jihar Jigawa.

 

Karanta: Cin Amana: Mijina Ya Man Duka Don Ban Gaida Amaryarsa Ba – Uwargida Ta Fadawa Kotu

 

Alhaji Kabiru Ali ya yi kira ga kananan hukumomi 23 daga cikin 27 da su yi koyi da ragowar hudu wajen dawo da awakin da raba a kashin farko domin wasu su amfana.

 

Karanta: Matsafa Sun Yiwa Wasu Kananan Yara Yankar Gunduwa-gunduwa

A jawabinsa sakataren kwamitin rabon awaki na jiha Dr Salisu Abdullahi ya yi kira ga kananan hukumomi dasu cigaba da baiwa kwamitin cikakken hadin kai da goyan baya domin samun saukin gudanar da aiyukan kwamitin

Leave A Reply

Your email address will not be published.