GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Shekaru Ko Tsufa Bai Hana Saduwa Tsakanin Namiji Da Mace Sai Dai Idan Mutum Raggo Ne – Binciken Masana

Shekaru Ko Tsufa Bai Hana Saduwa Tsakanin Namiji Da Mace Sai Dai Idan Mutum Raggo Ne – Binciken Masana

116

- Advertisement -

Kamar yadda aka sani ne da zaran shekaru sun ja ko kuma mutum ya manyanta hakan kan sanya mutum ya kasa yin wasu ayukkan da ya saba a lokacin da ya ke matashi, daya daga cikin wadannan abubuwa sun hada da jima’i da ayyukan da dama masu bukatar amfani da karfi.

 

Karanta wannan: Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Gina Masallatan Kamsisalawati 1,689

 

Masana a bangaren ilimin kiwon lafiya da kuma wasu mutane da dama su kan alaka nasaban da tsufa.

Wasu masu bincike daga jami’ar Keele dake kasar Britaniya sun bayyana cewa akwai kanshin gaskiya a zancen sai dai kuma ba kowani lokaci bane hakan ke faruwa da mutum.

Dana Rosenfeld wacce itace jagoran wannan bincike ta bayyana cewa duk da haka akwai yadda mutum ya gudanar da rayuwar sa alokacin da yake da kuricciya.

 

Karanta wannan: Tsoho Dan Shekaru 50 Ya Yiwa Wata Budurwar Fyade A Jihar Gombe

 

Wadannan canfe –canfe sun hada da:

1. Rashin son yin juma’i idan an tsufa

Rosenfeld ta bayyana cewa rashin son yin juma’I idan an tsufa ya danganta da irin halin rayuwar da mutum ya yi amma ba tsufa ne ke kawo hakan ba.

2. Rikicewa da tsofaffi ke yi

Ta ce kwakwalwar mutum na rikicewa ne idan mutum na yawan tunani tun yana da kurucciya wanda koda ya tsufa yake rikicewa.

Sannan ingancin kula da kiwon lafiyar da mutum ya samu yana da nasaba da yanayin rikicewarsa a lokacin da ya tsufa.

3. Tsufa na sa mutum rashin yin magana da walwala

Rosenfeld ta bayyana cewa rashin yin magana ko kuma fara’a da mutane ya danganta da yanayin mutum amma ba tsufa ne ke kawo hakan ba.

Misali wasu tun farkonsu Allah ya yi su ne ba masu son mutane ba ko kuma ba masu son hulda da mutane ba sannan kuma wasu Allah ya yi su masu son mutane.

 

Karanta wannan: Dalilin Da Ya Sa Na Yiwa Mahaifiyata Tare Da Surukata Fyade – Inji Wani Manomi

 

Shi yasa ake ganin cewa wasu tsofaffin duk da tsufan su suna da kokarin yin zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki.

4. Tsufa na kawo rashin karfin garkuwan jiki

Rosenfeld ta ce hakan ya danganta ne da ingancin kiwon lafiyar mutum wanda ya hada da halin rayuwarsa, kula da irin abincin da ke ci.

Misali tafiya ko kuma aikin da wasu tsofaffin dake kauyen mu yara baza mu taba iya yin shi ba duk da cewa mu yara ne.

Leave A Reply

Your email address will not be published.