GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Shugaban Ƙasa Buhari Zai Ƙaddamar Da Yaƙi Da Yin Fitsari Da Kashi Barkatai

Shugaban Ƙasa Buhari Zai Ƙaddamar Da Yaƙi Da Yin Fitsari Da Kashi Barkatai

20

- Advertisement -

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da yaki da yin ‘kashi da fitsari’ barkatai a fadin Najeriya.

Karanta: RAMADAN: Lokacin Da Yafi Daucewa A Yi Sahur

An saka wa yaki da ‘fitsari da kashi’ a bainar jama’a suna ‘domin tsaftace Najeriya, yi amfani da bandaki (Clean Nigeria, Use Toilet)’, sai dai ba a sanar da lokacin da shugaban kasa zai kaddamar da hakan ba.

Yin hakan na daga cikin kokarin gwamnati na kawo karshen yaki da yin ‘fitsari da kashi’ a fili zuwa karshen shekarar 2025.

Akalla mutane miliyan 47 ne ke yin bahaya a filin Allah a Najeriya, kamar yadda bincike ya nuna. Kananan hukumomi 10 ne kacal daga cikin 774 dake Najeriya aka bayyana a matsayin wadanda ba a yin bahaya a fili a yayin da Buhari ya kaddamar da shirin tsaftar muhalli.

Ministan albarkatun ruwa na kasa, Sulaiman Adamu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya, wanda aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace ” Mun dauki wasu matakai domin tabbatar da tsaftar muhalli yayin tattaunawar mu kafin ranar da shugaba Buhari zai kaddamar da yaki da yin bahaya a fili, wanda aka yiwa lakabi da ‘domin tsaftace Najeriya, yi amfani da bandaki’

“Shugaban kasa da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa zasu kasance wakilan tabbatar da tsaftace muhalli a fadin Najeriya da kuma tabbatar da samun nasarar shirin da shugaban kasa zai kaddamar.

Karanta: Kwankwaso Jahili Ne Ko Sharar Masallaci Bai Chanchanta Ya Samu Ba Bare Shugaban Ƙasa – Inji Dr Isah Ali Pantami

“Mun nemi kudi N10.6 domin tabbatar da nasarar shirin, ba iya gwamnati ce kadai zata samar da kudaden ba, kungiyoyi daa kamfanoni zasu bayar da gudunmawar kudin da za a yi amfani da su wajen yin amfani da jaruman fim, matasa, yara da mata wajen wayar da kan jama’a a kan illolin yin bahaya a fili da muhimmancin tsaftar muhalli,” a kalaman ministan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.