GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Siyasar Kaduna: Sheik Gumi Ya Fara Zama Abun Tsoro Ga Musulmai

Siyasar Kaduna: Sheik Gumi Ya Fara Zama Abun Tsoro Ga Al'ummar Musulmin Nijeriya

55

- Advertisement -

 

Mun dade muna fada wa mutane cewa Dafta Ahmad Gumi ba Malami bane mai kishin addini da kuma cigaban talaka, yanzu ko kunya bai ji ba ya bude baki yana nuna wa mutane cewa zaben da El-Rufa’i Yayi na Musulma a matsayin mataimakiyar gwamna ba dai dai bane, wai dole suma Kiristoci ayi musu adalci a basu mataimakin gwamna idan baza su samu gwamna ba.

 

Karanta wannan: Shekaru Ko Tsufa Bai Hana Saduwa Tsakanin Namiji Da Mace Sai Dai Idan Mutum Raggo Ne – Binciken Masana

 

Wannan yana nuna baka fahimci littafin da kake karantarwa mutane ba na (As-siyasatul shari’a) baka San me Musulunci yake nufi da adalci ba, adalcin turawa ne kake so ka mayar dashi adalcin Musulunci, kuma baza su taba hadu ba har abada.

wannan wane irin wawanci ne haka wai kai Malam, kaje jihar Filato Musulmi sun kai kashi 50 ko sama da haka, an basu mataimakin gwamna? jihar Benue ma haka, Taraba da sauran su, dama malam Al-baniy Zaria ya fada mana kai dan bidi’a ne kuma ba Malami bane

Kuma wallahi Kungiyar Izala kuma kuna da laifi, kuna kallon irin ta’adi da barnar da yake yi amma baza ku tsawatar masa ba? ko kuma Ku hana shi wa’azi a Masallacin Sultan Bello, kawai don shi ‘dan malam ne yasa baza a fada masa gaskiya ba? to wallahi kuji; ba’a yin sunnah da munafunci, ba’a yin sunnah da rufa asirin 6ata gari.

 

 

Karanta wannan: Kisan Janar Alkali: ‘Yan Sanda Sun Cafke Matar Da Ta Jagoranci Zanga-Zangar Hana Yashe Kogin ‘Dura-Du’

Sheikh Bala Lau ka fito ka dauki mataki, muna maka kyakkyawan zato kai mutumin kirki ne kayi abinda ya dace, ku hana shi wa’azi a duk inda yake da alaka da Izala shike nan, Salafiyya kuma ko a mafarki bai isa ya tinkari wurin su ba.

 

Manufar Ahmad Gumi shine ya faranta wa mai gidan sa Atiku Abubakar koda kuwa hakan zai fusatar da dubban Musulmi, ko Allah bazai so ba shi zai yi, idan har shi Ahmad Gumi Malamin Allah ne ya kamata yayi murna ne da abinda El-Rufa’i yayi, saboda na tabbata Ahmad Gumi yana daga cikin wadanda suka San illar da Ibrahim Yakowa yayi wa Musulmin Arewa bama Kaduna ba a ‘yan kwanakin da yayi a mulkin Kaduna, kafin Allah ya kifar dashi a jirgin sama a 2012.

 

Kuma ka duba ka gani anyi rikici a Kaduna a kwanakin nan an sanya dokar ta baci (curfew) gwamna El-Rufa’i ya rinka yawo cikin dare da rana yana yawo da kafan sa yana daukan matakin zaman lafiya, amma duk da haka Ahmad Gumi baka fito ka yaba masa ba saboda yana APC ko?

Babu abinda yake fitowa a bakin ka sai sharri? sai gazawar Musulmi? alkhairi bazai fito daga bakin ka ba, haka Manzon Allah yake? kullum fadan kuskuren Masu mulki yake yi? gaskiya baka san ciwon da yake damun Musulmi a yau ba.

Yanzu kuma zaka ga wasu wawaye jahilan mabiyan sa ko daqiqan ‘yan PDP sun fito suna nuna abinda ya fada dai-dai ne, suna yaba masa suna yiwa maganar tashi tagomashi.
Na rantse da Allah duk wanda yayi adawa da El-Rufa’i akan batun bayar da mataimakin gwamna wa Musulmai yana da mummunar manufa akan Musulmi ko waye shi.

 

 

Karanta wannan: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gabatar Da Wadanda Suka Kashe Janar Alkali (Hotuna)

 

Bamu hana ka kayi adawa da El-Rufa’i akan wasu abubuwa naka ba, amma rashin hankali ne da kuma dabbanci kayi adawa dashi akan bayar da deputy wa Musulmai, dan haka matasa da sauran jama’a kada Ku rudu da abinda wannan Ahmad Gumi yake fada, babu kishin sunnah a tare dashi balle Musulunci, dan bidi’a ne na karshe, kuma duk sadda yayi katobara zamu bayyana wa mutane yadda abin yake ko a Facebook ko akan minbari.

Abinda El-Rufa’i yayi dai dai ne kuma Allah ya saka masa da alheri ya tsare shi daga Malaman dollar da commercial Sheikhs…

Marubuci: Abdulhadi Isah Ibrahim .

Madogari: Datti Assalafiy

Leave A Reply

Your email address will not be published.