GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Babban Hadimin Ganduje Ya Ajiye Aikinsa Sabo Da Gwamnan Ya Ƙi Karɓar Ƙaddara

Babban Hadimin Ganduje Ya Ajiye Aikinsa Sabo Da Gwamnan Ya Ƙi Karɓar Ƙaddara

30

- Advertisement -

Dakta Hashim Suleiman Dungurawa babban hadimin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje akan ƙawata birane, ya yi murabus daga kujerarsa bisa zargin ƙin rungumar ƙaddara da gwamnan yayi akan sakamakon zaɓen ranar Asabar.

 

Karanta: Tattalin Arziki: ‘Yan Kasar Indiya 50,000 Suke Gudanar Da Harkokin Kasuwanci A Najeriya

 

Hashim Suleiman ya gabatar da takardar murabus ɗinsa ne ga sakataren gwamnatin jihar Kano a jiya Laraba, 14 ga watan Maris. Cikin wasikar da ya aikewa gwamnan ya godewa gwamnan da damar da ya bashi na bautawa jihar Kano.

 

Karanta: Gargadi: Masu Fama Da Ciwon Ido Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa – Masana

 

Ya kuma bayyana cewa babban dalilin yin murabus din na sa shi ne rashin rungumar ƙaddarae da Ganduje ya gaza yi bayan ya bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya lashe zaɓen.

 

Ya ƙara cewa Abba Gida Gida ya lashe zaɓen amma hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC ta ƙi kammala zaɓen.

 

 

Karanta: Bai Kamata INEC Ta Fake Da Cewa Zabe Bai Kammala Ba Kawai A Rika Yiwa Jama’a Wala-Wala – Sunday Karimi

 

A ƙarshe ya ce a matsayin Ganduje na Khadimul-Islam, ya kamata ya haƙura saboda hakan ya zama darasi ga wasu Musulmai masu bautar Allah da iklasi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.