GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Siyasar Kano: Dalilina Na Son A Sake Zaben Gwamna Ganduje – Inji Sheik Kabiru Gombe

Siyasar Kano: Dalilina Na Son A Sake Zaben Gwamna Ganduje - Inji Sheik Kabiru Gombe

547

- Advertisement -

 

Sheik Kabiru Gombe ya yi kira ga al’ummar jihar Kano akan su sake zaben Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano karo na biyu.

 

Malam Kabiru Gombe ya ce Allah ma ya sani yana da dalilin da ya sa ya ce a sake zaban Ganduje a matsayin gwamnan jahar Kano kuma yana kyautata zaton Allah ma zai yadda da dalilin shi.

 

Karanta: Siyasar Kano: Tsakani Da Allah Talakawan Kano Abba Suke So – Abdulmumini Kofa

 

Malam Kabiru Gombe ya fadi kadan daga cikin dalilin da ya sa yace al’umma su sake zaben Ganduje.

 

Sheik Kabiru Gombe ya ce kaf Nijeriya babu wani Gwamna da yake kan kujerar Gwamnan ya tsaya musuluntar da Maguzawa sai Ganduje.

 

Malam Kabiru Gombe ya kara da cewa Ganduje ya musuluntar da Maguzawa sama da dubu 20.

 

 

Karanta: Ba Gaskiya Ba Ne Cewa Za Mu Sake Shiga Wani Yajin Aiki – ASUU

 

Malam Kabiru Gombe ya ce kwanakin baya Ganduje ya gayyace su jihar Kano domin su Musuluntar da Magujawa dari biyu.

 

Wallahi Saida yayi kuka domin ya ga abinda bai taba gani ba.

 

Malam ya kara da cewa “abinda zai kara birge ka shine duk wanda Ganduje ya musuluntar sai ya bashi sana’a domin ya tsayu da kafafunsa.

 

 

Karanta: Gargadi: Masu Fama Da Ciwon Ido Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa – Masana

 

Shehin Malamin ya fadi hakan ne a wani bidiyo a lokacin da ya amsa gayyatar da Gwamna Ganduje ya yi masa na musuluntar da Maguzawa a Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.