GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Siyasar Kano: Mataimakin Ganduje Ya Mika Takardar Hakura Da Aiki

Siyasar Kano: Mataimakin Ganduje Ya Mika Takardar Hakura Da Aiki

194

- Advertisement -

Mai taimaka wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje kan harkar tsara birane, Hashim Dungurawa, ya mika takardar hakura da aiki da gwamnatin inda ya ce zai koma jam’iyyar PDP.

 

Dungurawa ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da aiki da jam’iyyar gwamna mai ci ba sannan ya gode wa gwamnan bisa damar da ya bashi na yin aiki tare da shi. Tuni ya kammala shiri tsaf domin komawa jam’iyyar PDP.

 

Karanta: Duk Da Taron Dangi Sai Da Kwankwaso Ya Kai Gwamnatin Ganduje Ƙasa A Kano – Nasiru Sule Garo

 

Idan ba a manta ba jihar Kano na daga cikin jihohin da za a gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Maris.

 

Sauran jihohin da ba a kammala zaben gwamnan ba sun hada da Jihar, Filato, Bauchi, Adamawa, Sokoto da jihar Benuwai.

 

Karanta: Wasu Mahara Sun Kashe Mutane 22 A Birnin Gwari, Kaduna

 

A jihar Kano abin yayi zafi da sai da aka rika kai ruwa rana tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun da ke fafatawa a zaben, wato APC da PDP.

 

A dalilin haka sai da ‘yan sanda suka tsare mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna da kwamishinan Kananan hukumomin jihar, Sule Garu. Daga baya an sake su.

 

Karanta: Za Muyi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Siya Da Siyar Da Kuri’ar Su a Kano – ‘Yan Sanda

 

A sakamakon da aka riga aka bayyana, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’u sama da Miliyan daya.

 

An bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta baiwa APC rata shine ya sa zaben bai kammalu ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.