GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Sojoji Sun Ƙwace Mulki Daga Hannun Omar Hassan Al-bashir Na Sudan

Sojoji Sun Ƙwace Mulki Daga Hannun Omar Hassan Al-bashir Na Sudan

29

- Advertisement -

 

 

Dakarun sojin ƙasar Sudan sun kewaye gidan Talabijin na kasar tare da shiga cikinsa.

Tashar Talabijin ta Almayadeen ta bayyana cewa, sojojin sun hambarar da Shugaba Umar Al-Bashir da gwamnatinsa.

 

Karanta: Dandazon Ƙudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Hukumar Kwastan

 

An bayyana cewar nan da wani ɗan loakci sojojin na Sudan za su fitar da sanarwa ta musamman.

Majiyoyin siyasa kuma na cewa, tuni aka fara kama shugabannin jam’iyyar NCP mai mulki a Sudan.

Haka zalika an hana tashin jiragen sama a Khartoum inda ake bayar da izinin sauka kawai.

 

Karanta: EFCC: Kotu Ta Baiwa Shekarau Iznin Tafiya Umara

 

A ranar 19 ga watan Disamban 2018 aka fara zanga-zanga a Sudan bayan kara farashin kudin burodi inda aka fara zanga-zanga a garuruwan Atbera da Port Sudan dake gabar kogin Nil, cikin kankanin lokaci zanga-zangar ta mamaye fadin kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.