GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 23, sun cafke 18, tare da kubutar da mutane 40 a Zamfara

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 23, sun cafke 18, tare da kubutar da mutane 40 a Zamfara

66

- Advertisement -

Rudunar sojin Nijeriya da ke gudanar da ayyukan atisayen Sharan Daji a jihar Zamfara, sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda guda 23 tare da cafke wasu guda 18, wadanda ake zargi da ayyukan laifin ta’addanci daban-daban da suka hada da satar shanu, garkuwa da mutane, samar da bayanai ga ‘yan ta’adda da kuma samar da kayan aiki ga ‘yan ta’adda.

 

Karanta: Shikenan Dangote Ya Bayayyana Sirrin Yadda Zakayi Ka Samu Kudi A Duniya……Karanta Kasha Mamaki

 

Kakakin rundunar atisayen Sharar Daji, Manjo Clement Abiade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Juma’a, inda ya bayyana cewa rundanar tasu ta yi luguden wuta ta sama a kan dazukan Kagara, Gando, Fankama, Fete da Dumburum. Cikin wadanda aka kama har da wani Muhammadu Iso, wanda ya yi fice a harkar garkuwa da mutane.

 

An kama Muhammadu Iso ne a kan iyakar Nijeriya da Nijar sakamakon hadin gwiwar tsaro da ke tsakanin kasashen biyu.

 

Karanta: Cututtukan Da Tafasasshen Ruwan Albasa Ke Magancewa

 

Muhammadu Iso dan asalin garin Naagwalam ne da ke jihar Katsina, kuma ya kware wajen aikata fashi da makami da garkuwa da mutane a kan titin Batsari zuwa Jibiya.

 

 

Haka kuma, rundunar sojin ta yi nasarar kubutar da mutane 40 da masu garkuwa da mutane suka rike da su a cikin daji da suka hada da manyan mutane maza da mata da kananan yara a jihar Zamfara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.