GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Mahara 21, Sun Cafke 17 A Zamfara Da Katsina

Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Mahara 21, Sun Cafke 17 A Zamfara Da Katsina

27

- Advertisement -

Jami’in rundunar sojin Najeriya Clement Abiade ya ce dakarun sojin Najeriya sun kashe mahara 21, sannan sun kamo 17 a wani farmaki da suka kai maboyar ‘yan ta’addan a dazukan dake iyaka da Jihohin Zamfara da Katsina.

 

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Abia

 

Bayan haka kuma dakarun sun ceto mutane 89 da aka yi garkuwa da su a jihohin Zamfara da Katsina.

 

Abaide ya sanar da haka ne ranar Talata inda ya kara da cewa rundunar ta kai wannan farmaki a ne tsakanin ranakun 22 da 28.

 

Karanta: Wata Budurwa Ramatu Tafida ‘Yar Shekaru 17 Ta Yanke Mazakutar Saurayin Da Zai Aureta a Jigawa

 

Ya kuma ce masu garkuwan sun tsare 55 daga cikin mutanen da suka sace ne a karamar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara.

 

Bayan haka Abaide yace rundunar ta kama wasu mutane biyu da maharan wajen kawo musu rahotanni kafin su kai hare-hare.

 

Karanta: Amfanin Ganyen Kuka Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

Wadanda aka kama sune, Musa Amadu da Auwalu Mutairu a haka yanzu suna nan suna tsare ana tuhumar su da samun bayanai daga wurin su.

 

Abaide yace an rasa rayukan faran hula 11 da dan banga daya a dalilin arangamar da rundunar ta yi da maharan.

 

Karanta: ‘Yan Taraba Sun Yi Wa Gwamnansu Korar Kare

 

” Ina kuma so in shaida muku cewa maharan sun sace mutane shida ne a kauyen Asoula dake karamar hukumar Tsafe ba a Birnin Magaji ba kamar yadda wasu gidajen jaridun ke yadawa cewa sun fi haka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.