GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Soyayyar Facebook: Budurwar ‘Yar Shekaru 22 Ta Kwacewa Saurayinta Mota a Haduwarsu Ta Fari

Soyayyar Facebook: Budurwar 'Yar Shekaru 22 Ta Kwacewa Saurayinta Mota a Haduwarsu Ta Fari

23

- Advertisement -

 

Wata budurwa mai shekaru 22 da haihuwa da aka bayyana sunanta da Sandra ta kwace motar saurayinta kirar Toyota RAV4 2011 mai lamba KTU 311.

Majiyarmu ta gano cewa wannan saurayi da ba a bayyana sunansa ba yana zaune ne a rukunin gidaje na Oganiru da ke birnin Awka, jihar Anambra.

Bayanai sun zo mana cewa Sandra ta hadu da saurayin nata ne a dandalin Facebook, kuma suka ci gaba da tadi, lamarin da ya rikide zuwa soyayya.

Daily Post ta rawaito cewa Sandra daya ce daga cikin wasu ‘yan fashi 4 da suke yin amfani da ita Sandrar wajen yaudarar maza suna yi musu kwace.

Sandra ta gayyaci masoyin nata mai shekara 30 wanda majiyarmu ta gano cewa dan Kasuwa ne, ta yi musu wajen haduwa a makarantar firamare ta St Vincent da ke a unguwar Ogidi, a karamar hukumar Idemili ta arewa.

Bayan haduwarsu ne sai wasu maza 3 dauke da makamai suka yi wannan saurayi dirar mikiya suka karbe motarsa da wasu kayan kudi da ke a jikinsa suka tafi tare da budurwar tasa suka bar shi yana ta burari.

Kakakin ‘yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Muhammed ya bayyana mana cewa ‘yan sun yi nasarar samun motar da barayin suka sace bayan da suka bi bayan barayin.

Sai dai Sandra da abokan fashinta sun fice daga motar sun ranta a na kare sun kude cikin surkukin daji.

Zuwa yanzu dai ‘yan sanda na ci gaba da bincike don gano wadannan nan bata gari, Sandra da tawagarta

Leave A Reply

Your email address will not be published.