GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Tattalin Arziki: ‘Yan Kasar Indiya 50,000 Suke Gudanar Da Harkokin Kasuwanci A Najeriya

Tattalin Arziki: 'Yan Kasar Indiya 50,000 Suke Gudanar Da Harkokin Kasuwanci A Najeriya

16

- Advertisement -

Babban jakadan Nijeriya a kasar Indiya, Mista Abhay Thakur ya bayyana cewa akalla ‘yan asalin kasar Indiya 50,000 ne suke gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya, akwai kwararru a fannoni daban daban, akwai wadanda suka zuba hannayen jari, akwai likitoci da injiniyoyi da ma malaman makarantu da sauransu masu yawa.

 

Karanta: Zamu Gudanar Da Zaben Gaskiya Da Gaskiya A Jahar Kano – INEC

 

Thakur ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, kasar Indiya ita ce babbar abokiyar kasuwancin Nijeriya, inda huldar cinikayya a tsakanin kasashen biyu ta kai dalar Amurka biliyan 12, sai kuma kamfanonin indiya da suka sanya hannun jarin da ya kai dalar amurka biliyan 10.

 

Karanta: Ko Da Tsiya Sai APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Kano – Inji Shugaban APC Na Jihar Kano

 

Kasar Indiya ta yi matukar taimakawa ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, sannan kasar Indiyan ita ce kasar da take kan tsarin dimokradiyya da ta fi ko wacce girma a duniya, kasar ta na da masu zabe da suka kai miliyan 900, inda ita kuma Nijeriya ita ce kasar da tafi ko wacce yawan al’umma a nahiyar Afrika, wannan dalilin ya sa kasashen biyu suke da hulda mai kyau a tsakaninsu

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.