GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Tsafi: Wani Matashi Ya Sace Dan Kamfen Matar Yansa Da Kanwarsa

Tsafi: Wani Matashi Ya Sace Dan Kamfen Matar Yansa Da Kanwarsa

50

- Advertisement -

Wani matashi mai kimanin shekaru 25 da haihuwa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan an same shi da laifin sace dan tofin matar dan uwansa da na kanwarsa.

Matashin mai suna Ojonugwa Adejoh ya gurfana ne a shedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo tare da wani malamin addinin Kirista, Olajide Ogunleye mai shekaru 53, na cocin Celestial da ke a garin Uso a karamar hukumar Owo, jihar Ondo.

 

Karanta: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i (Shawara Ga Maza)

 

‘Yan sanda sun cafke wadanda a ke zargin ne bayan da matar dan uwan matashin ta kama kanin mijin nata a lokacin da ya ke kokarin yin awon gaba da dan tofin nata kuma bata yi kasa a gwiwa ba ta sanar da ‘yan sanda.

Matashi Ojonugwa ya tabbatar da aikata laifin inda ya kara da cewa malamin majami’ar ne ya gusar da hankalinsa kafin ya tura shi ya debo masa wandunan a lokacin yana kan hanyarsa ta tafiya wajen aikinsa.

“Na dakata a wajen limamin majami’a don ya yi min addu’ar samun nasara domin dai bana ganin ci gaba a sana’ata.

 

Karanta: Illar Ruwan Tsarkin Bayan Gida Idan Ya Taba Al’aura (Shawara Ga Mata)

 

“Ko da na fada masa haka, sai ya tambaye ni wace iriyar sana’a nake yi? Na fada masa ina aikin gyara bodin mota ne (panel beater). Sai ya umarce ni da miko tafin hannaye na don ya yi min addu’a. Ko da mika masa hannuna sai ya bani wani abu ya ce na hadiye, sannan ya yi min addu’a, kana ya umarce ni da na tafi.

“Amma ko da na isa gida, sai na fita daga hayyacina, inda a wannan yanayi ne na dauki wandunan matar yayana da na kanwata na kai wa limamin majami’a.

“Ni ban dauki wandunan da nufin gabatar da wani sihiri ko tsafi ba.

 

Karanta: Hukumar INEC Ta Gano Mazabu 24 Da Zabe Ba Zai Iya Yiwu Ba A Jihar Yobe

 

“Wanduna biyar na dauka, biyu na matar yayana, guda uku na kanwat,” inji Ojonugwa..

Sai dai limamin majami’ar ya musanta zargin, inda ya ce sharri ne kawai Ojonugwa da dan uwansa ke son yi masa saboda ya ki basu hayar filinsa.

Kakakin ‘yan sandan jihar Ondo, Femi Joseph ya tabbatar da cewa ‘yan sanda na ci gaba da aiwatar da bincike game da dalilin sace wandunan, sannan ya yi gargadi ga mata da su kara adana dan tofinsu domin tsira daga azzalumai da mugun nufinsu.

 

Karanta: Abubuwa Da Su Ka Sa Na Ke Goyon Bayan Atiku – Obasanjo

 

“Muna amfani da wannan dama wajen yin gargadi ga mata da su kiyaye sosai wajen adana wandunansu sakamakon wannan annoba da ake fama da ita na satar dan kanfai don yin sihirin arziki.

Ya zama wajibi iyaye su kula tare da jan hankalin ‘ya’yansu mata kan kula da dan tofinsu don tsira da ransu da lafiyarsu,” inji Kakakin ‘yan sandan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.