GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

U-Report: Bayanin Wasu Malamai A Kan Bikin Maulidi

U-Report: Bayanin Wasu Malamai A Kan Bikin Maulidi

21

- Advertisement -

Annabi s.a.w shine yafi kowa tsoran Allah da yi masa biyayya haka zalika bai taba sabawa Allah ba. Annabi s.a.w shine jagoran duk wani mai tsoran Allah limamin masu ayyuka na kwarai,

 

Karanta wannan: Cutar Damuwa: Ma’aikacin Banki Ya Kashe Kanshi Kan Kunshi (Hotuna)

 

Dole ne son annabi ga ko wacce halitta, domin son annabi shine son Allah idan kana son annabi kana son Allah idan baka son annabi baka son Allah, Allah ne ya sanya mana annabi ya zama abinda zamuna koyi dashi a cikin dukkanin rayuwar mu,

 

Hatta shiga bandaki, da shan ruwa gaba daya mun samu tarbiyya ne daga gare shi, Kai!! Hatta yadda ake mu’amala ta iyali sai da aka rawaito daga annabin kan shi da matan shi suna koyar da yadda ake yi kuma kowa yana koyi da wannan sunnar domin amfanuwa da samun jin kwanciyar hankali,

 

Karanta wannan: Dalilin Da Yasa Muka Bulo Da Shirin Raba Awaki – Gwamnatin Jihar Jigawa

 

Dan haka babu wani abu wanda yake a cikin rayuwar annabi s.a.w wanda ba al’qur’ani bane domin an tambayi matar shi nana Aisha cewa mene ne dabi’un manzon Allah sai tace (Dabi’un shi shine al’qur’ani) sannan a wani hadisin aka kara tambayar ta sai ta karanta ayoyi guda goma na farkon suratul momin bayan ta gama karantawa sai tace(Ha’kaza kuluqu (rasulullahi s.a.w) haka dabi’un annabi s.a.w suka kasance,

 

Dan haka wadannan bayin Allah sune suka rayu da manzon Allah a cikin kunci domin a rayuwar su babu jin dadi illa kawai kasantuwar su da annabi s.a.w shine jin dadin zuciyoyin su, Wadannan mutane sune almajiran annabi s.a.w haka zalika sune malaman al’ummar shi kuma sunfi kowa iya addini da kwatantawa yadda Allah yace dan haka a cikin sune kadai zaka samu yadda za’a koya maka addini.

 

Karanta wannan: Wasu Jiga-jigan Jam’iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC

 

Kuma sun fika son Allah da manzon shi Allah ne shedar su akan hakan, Dan haka duk wani abu da wani wanda bai samu shedar cikar imani ba zai kawo da sunan addini ko soyayya wanda ya saba musu kuma ya sabawa koyarwar su toh babu ahakka rudune da kawatar shedan,

 

Cin fuskar annabi ne da sahabbai kace maulidi addini ne, Kiyayya ne ga annabi kace akwai bidi’a mai kyau wacce.

 

Daga: Aliyu Sani Abdu Utai

Leave A Reply

Your email address will not be published.