GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Uwar Jiki: Alaƙar Ciwon Gwiwa Da Kiba

Uwar Jiki: Alaƙar Ciwon Gwiwa Da Kiba

27

- Advertisement -

Ɗaya daga cikin matsalolin da masu ƙiba ko teɓa ke fuskanta akwai haɗarin kamuwa da ciwon gwiwa.

Sai dai rage ƙiɓa na faruwa ne a yayin da mutum ya ɗauki wani daga cikin tsarikan rage teɓa ko ƙiba; kamar daidaita salon cimaka, ko kuma ɗaukar tsararren atisayen da ke temakawa wajen rage ƙiba.

 

KARANTA: Zaben Gwamnoni: Hon. Abdullahi Ya Sake Kira Ga Al’ummar Mazabarsa Da Su Kauracewa Rikicin Zabe

 

Haka nan kasancewar gaɓar gwiwa ita ce ke ɗauke da dukkan nauyin mutum tun daga kai har zuwa gwiwa, wannan yasa gaɓar ke da mafi haɗarin zaizayewar gurunguntsin gaɓa. Kuma zaizayewar gurunguntsi da ƙanƙancewar majinar gaɓar ne ke kawo ciwon gwiwa da ake cewa “Amosanin gwiwa” ko kuma “Knee Osteoarthritis” a turance.

 

Karanta: Asiri: An Gano Sunan Gwamna El-rufai Kulle Cikin Likkafani A Makabarta (Hotuna)

 

Saboda haka gwargwadon rage teɓa gwargwadon raguwar nauyin da ke kan gwiwa; kuma gwargwadon raguwar haɗarin kamuwa da ciwon gwiwar.

A taƙaice dai, yawan nauyin kilogiram ɗin da mutum ya rage to yawan samun sauƙin gaɓar gwiwa kenan yayin da mutum yake a miƙe, a tafe, ko yayin gudu.

 

Karanta: An Kama Kasurgumin Dan Ta’addan Dake Haddasa Rikicin Garin Kasuwar Magani A Kaduna

 

Idan kana da ƙiba temakawa gwiwarka yau domin kaucewa ciwon gwiwa gobe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.