GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Uwar Jiki: Ciwon Wuya

Uwar Jiki: Ciwon Wuya

14

- Advertisement -

A ƙoƙarin bankuna da asibitoci na tabbatar da rufe sirrin abokan hulɗa da marassa lafiya yayin aiki da kwamfuta ta kai su ga amfani da wani nau’in tebur da ke ɓoye fuskar na’urar kwamfutar ta yadda wanda ke gefe ba zai iya hangen bayanan da suka bayyana a fuskar kwamfutar ba.

 

Karanta: Wani Karamin Yaro Dan Shekara Biyu Ya Fada Rijiya A Kano

 

Sai dai bayan rufe sirri da wannan tebur ya zo da shi, a hannu guda kuma likitocin Fisiyo sun bayyana matsalar amfani da irin wannan tebur wajen kawo ciwon jiki musamman ciwon wuya da ciwon baya.

 

A yayin aikin da irin wannan tebur ma’aikaci sai ya sunkuyar da kansa kimanin digiri 35 zuwa ƙasa kafin ya iya duba fuskar kwamfutar.

 

Sai dai kasan nauyin kan mutum ya kai nauyin kilogiram huɗu zuwa biyar?

 

Karanta: Siyasar Kano: Zan Maida Abba Gida-Gida, Gida – Ganduje

 

Duk da wannan nauyi kan mutum ya daidaita ne saboda haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin ƙasusuwan wuya, tantanan da ke riƙe da ƙashi da ƙashi, da tarun tsokokin da suke aiki tare domin tsayar da kai a gurbinsa.

 

Sai dai nauyin kan mutum yana ninkawa yayin da mutum ya sunkuyar da kansa kimanin kowanne digiri goma sha biyar. Abin nufi a nan shi ne ninkawar nauyin shi ne ninkawar aiki ko wahalar da tantanai da tsokokin wuya suke sha wajen riƙe kan. Haka nan ƙarin wannan aiki ko wahala na jefa tsokokin shiga wasu ɗabi’u ko yanayi da za su haifar da ciwon wuya.

 

Karanta: Ina Kira Ga Masoya Na Suyi Hakuri Domin Nasara Na Tare Da Masu Hakuri – Abba K Yusuf

 

Yayin amfani da kwamfuta ko na’urar wasan yara a kan tebur tabbatar an daidai kujerar da teburin ta yadda kanka zai zama a miƙe yake ba tare da sunkuyawa ba. Wannan zai rage haɗarin samun ciwon wuya.

 

Domin haka kasance ka ɗaga fuskar na’urar sama daidai da ganinka maimakon sunkuyar da kai.

 

Karanta: Asiri: An Gano Sunan Gwamna El-rufai Kulle Cikin Likkafani A Makabarta (Hotuna)

 

Daga ƙarshe muna kira ga makarantu, ma’aikatu da bankuna da su ɗinga tintiɓar likitocin Fisiyo kafin samar da kujeru da tebura a wuraren aiki domin kaucewa jefa ma’aikata haɗarin samun ciwon baya da ciwon wuya wanda za a iya magancesu da shawarwarin da za su bayar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.