GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Wani Manomi Ya Horas Da Matasa 20,000 A Kan Sana’ar Kiwon Kaji Don Dogaro Da Kai (HOTUNA)

Wani Manomi Ya Horas Da Matasa 20,000 A Kan Sana'ar Kiwon Kaji Don Dogaro Da Kai (HOTUNA)

121

- Advertisement -

 

Wani manomin kaji Agric, Bilyaminu Almustapha, ya horas tare da da matasa maza da mata sama 20,000 a kan sana’ar kiwon kaji turawa  don dogaro da kai a Jos, jahar Filato, Najeriya.

 

Karanta:  Dan Majalisan Neja Ya Gina Gadaje, Da Tituna Tare Kwalbatai Da Asibitoci A Mazabansa (Hotuna)

 

Bilyaminu ya kasance mai gidan noman Mr. Biya Farms Nigeria Limited a birnin Jos. A matsayinsa na manomi sannan kuma dan kasuwa mai sana’ar noman kajin turawa wato Agric Chicken shi ya dauki nauyin wannan shirin da kansa ba tare da tallafi daga wurin gwamnati ba inda ya ce ya kaddamar da shirin ne domin shi ma ya bada na shi gudunmawan wajen rage yawan matasa marasa aikin yi a bisa kan layi

 

Ya gudanar da irin wadannan irin ne a kananan hukumomin 4 wadanda suka hada da kananan hukumomin  Bassa, da Barikin Ladi, da Mangu, da kuma Shandam a jahar Filato, inda aka horas da matasa a kan yadda za su yi kiwon kajin Agric.

 

A yayin da ya ke magana da manema labarai a kan shirin, Bilyaminu ya ce “an gudanar da shirin ne domin a horas da matasa a kan harkar sana’ar noman kajin Agric tare da fi’idarsa da kuma alheri da ke cikin ita wannan sana’ar. Shi wannan shirin zai taimaka wajen rage yawan matasa marasa aikin yi wanda sakamakon hakan ne ya kan su shiga kungiyoyi daban daban marasa amfani a gare su musamman ma kungiyar sara-suka sannan kuma domin a tallafawa tare da karfafawa matan mu na Arewa don su koyi sana’o’in hannu domin dogaro da kai.”

 

Karanta: Yadda Ake Amfani Da Kwai Wajen Maganin Karfin Mazakuta

 

Ya kara da cewa hakan zai taimakawa matasa wajen hanyar samun kudaden kansa wato halallin kudi tare da taimakawa tattalin arzikin jihar dama kasa baki daya.

 

 

A karshen shirin, kowane mutum daga cikin wadanda aka horas ya samu kaji 12, da kayan abincin kajin kilogaram 1.7, da kuma maganin kajin na wata 1 wanda hakan zai taimaka masu wajen aiwatar da abubuwan da suka koya a shirin kafin su samu jarin shiga kasuwancin.

 

Ga hotunan a kasa;

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.