GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Wani Matashi Ya Bukaci Kotu Ta Umurci Surukinsa Ya Biya Shi Kudin Sadakin Auren ‘Yarsa Da Ya Biya N340,000

Wani Matashi Ya Bukaci Kotu Ta Umurci Surukinsa Ya Biya Shi Kudin Sadakin Auren 'Yarsa Da Ya Biya N340,000

36

- Advertisement -

Wani matashi dan shekaru 32, Ahmed Sani, ya roki wata kotun shari’a da ke kauyen Magajin Gari a jihar Kaduna da ta taimake amsar kudi naira N340,000 hannun mahaifin yarinyar da ya so ya aura a matsayin sadaki

 

Sani ya fadawa kotun cewa surukinsa, Malam Alhassan, ya biya shi kudinsa saboda ‘yarsa ta ki aurensa.

 

Karanta: Dan Sanda Ya Harbe Wani Sojan Sama Har Lahira (Hotuna)

 

Matashin ya fadawa kotun cewa ya neme auren Sumayya Alhassan a wurin mahaifinta (Alhassan), wanda ya ba shi damar yin hakan sannankuma ya bukaci ya biya N20,000 a matsayin kudin sadakin ‘yarsa banda wasu kudade da ya kashe.

 

 Sani ya ce abun ya razana shi a lokacin da Malam Alhassan ya dakatar da dauren auren “don na kasa samarwa ‘yarsa gidan zama. Bayan na biya kudin sadakinta da kuma sauran kudaden da ya kamata na biya kamar yadda al’ada ya tsara wanda idan aka hada za su kai naira N340,000, na dauke ‘yarsa zuwa gidan da na yi haya amma daga baya ‘yar na sa ba ta so gidan ba” ya ce.

 

Karanta: Dan Shekaru 19 Make Da Kwayar Codeine Ya Dabawa ‘Yar Makwancinsa Wuka Har Lahira (Hotuna)

 

Ya roki kotun ta taya shi amsar kudin da ya kashe a hannun surukunsa saboda an hana shi matar.

 

Lauyar da ya ke kare surukin, Alhassan Aliyu, ya ce bayanin saurayin (Matashin) ba shi da wani asali inda ya bukaci kotun ta yi amfani da sashe 22 na dokar shari’ar jihar Kaduna, wanda ta bukaci a mayar da naira N100,000.

 

Karanta: An Yabawa Hukumar NPC Kan Yadda Ta Ke Gudanar Da Rajistar Haihuwa

 

Aliyu, ya roki kotun ta mika karar zuwa babbar kotun shari’a ko kuma ta yi watse da karar.

 

Alkalin kotun Malam- Dahiru Lawal, ya bukaci a mika karar zuwa babbar kotun shari’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.