GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Wani Mutum Ya Sace Shanu 150 Ya Yanka Guda 50 a Ciki

Wani Mutum Ya Sace Shanu 150 Ya Yanka Guda 50 a Ciki

22

- Advertisement -

An gurfanar da wani mutum mai suna Sanda Bakura a gaban kuliya a bisa zarginsa da sace shanu har guda 150, tare da yanka guda 50.

 

Karanta: Za Muyi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Siya Da Siyar Da Kuri’ar Su a Kano – ‘Yan Sanda

 

‘Yan sanda sun gurfanar da shi ne a gaban kotun majistare da ke Minna a yau Laraba.

 

Ana tuhumarshi da laifuka biyu da suka hada da makirci da sata wadanda suka saba da sashe na 97 da 287 na kundin dokar Penal Code.

 

Karanta: Ko Da Tsiya Sai APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Kano – Inji Shugaban APC Na Jihar Kano

 

Toh sai dai kuma Bakura bai amsa laifin ba a yayin da kotun ta karanto masa su.

 

‘Dan sanda mai kara ya roki kotun ta daga sauraran karar domin baiwa hukumar damar kara yin bincike.

 

Karanta: Dalilin Sake Zaben Gwamnan Jahar Kano Zagaye Na Biyu

 

Alkalin kotun, Mariam Kings ta bada belin Bakura akan Naira 100,000 tare da daga sauraran karar zuwa rabar 28 ga watan na na Maris.

Leave A Reply

Your email address will not be published.