GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Waraka 12 Da KUBEWA Ke Yi A Jikin Dan Adam

Waraka 12 Da KUBEWA Ke Yi A Jikin Dan Adam

73

- Advertisement -

AMFANIN KUBEWA

Hausawa na kiranta KUBEWA, Turawa na cewa LADY’S FINGER Amerikawa na ce GUMBO mutanen Spain na ce mata GUIBEIRO yayinda a India ake ce mata BENDAKAI. Amma dai duk an yi imanin cewar KUBEWA ta samo asali ne daga kasar Habasha wato Ethiopia da kuma Masar wato Egypt tun karni na 12. Mutane da dama na ci ko sham miyar kubewa saboda dadinta ne kawai amma ga kadan daga cikin amfaninta a matsayin magani wanda aka shafe shekaru dauruwa ana amfani da ita.A wasu kasashen Turai ma har packaging ake mata a matsayin magani.

 

Karanta: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i (Shawara Ga Maza)

 

1. Ana amfani da kubewa wajen maganin ciwon sugar wato Diabetes. Saboda abinda ake kira (fiber ) a cikinta, na amfani wajen daidaita yawan suga a cikin jiki, wanda kuma ke rage karfi ciwon sugar ko ma maganinsa.

 

2. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa kuma na sa jaririn ya girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so. Haka kuma jaririn da ke ciki zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa.

 

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Abia

 

3. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike daga jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun sun nuna nasarar rashin lalacewar koda musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar.

 

4. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon) wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki. Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar wani abu kamar majina ( Mucous membranes) na cikin babban hanji.

 

Karanta: Amfanin Ganyen Kuka Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

5. Kubewa na maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi.

 

6. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa.Yana kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace.

 

7. Yana matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yay i maka lahani ba. (blood coagulation).

 

Karanta: Hukumar INEC Ta Ce A Shirye Take Tsab Wajen Gudanar Da Babban Zaben Kasa

 

8. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa.

 

9. Wani sinadari a cikin kubewa da ake kira (soluble fibre) yana taimakawa wajen rage cholesterol wanda kuma hakan ke rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya sannan na taimakawa wajen samar da ingantaccen ruwan data (madaci) a hanji.

 

10. Amfani da kubewa a kai a kai na inganta kashin mace da namiji kuma na maganin dandruff. Za ka tafasa ruwa tare dayankakken danyen kubewa, idan yay i sanyi sai ka matse rabin lemon tsami a ciki sai ki rinka wanke kanki ko kanka da ruwan. Kuma yana kasha kwarkwata ma.

 

Karanta: Sojojin Nijeriya Sun Hallaka Mahara 21, Sun Cafke 17 A Zamfara Da Katsina

 

11. Kubewa na kara kare lafiyar garkuwan jiki ya kuma rage maka yawan kamuwa da cututtuka. Sinadaran Vitamin ce da calcium da magnesium da sauransu da ke cikin kubewa sukan taimaka wajen yaki da abubuwa marasa kyau a jikin mutum.

 

12. Kubewa na kara ingancin lafiyar ido da kuma hana kamuwa da yanar ido domin yana kunshe da Vitamin A da carotene masu yawa a cikinsa. Mai yawan shan kubewa zai iya tsufa da idanunsa garau.

 

Karanta: Samar Da Aiki: Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Sake Gudunar Da Shirin Rabon Awaki

 

YANDA AKE AMFANI DA SHI.

RUWAN KUBEWA.

A sa kubewa guda biyu zuwa uku (gudansa) a ruwa maras zafi ko dumi a cikin kwano ko gilashi a barshi ya kwana , sai a cire kubewar da safe a shanye ruwan. Kullun a rinka yin haka har kwanaki talatin ko fiye domin samun sakamakoo mai kyau. Ana iya cigaba da hakan.

 

Ko kuma a yankan kubewar a sanya cikin ruwa a barta ta kwana sannan a shanye ruwan kullun da safe. Amma za a dan ji daci daci.

 

Karanta: Wata Budurwa Ramatu Tafida ‘Yar Shekaru 17 Ta Yanke Mazakutar Saurayin Da Zai Aureta a Jigawa

 

Sannan ana iya mafani da wuka a fere kubewar wato bawonsa mai aunin kore sai a ci bawon kai tsaye danyensa amma kar ya wuce rabin cokalin shan shayi a lokaci guda.

 

Ko kuma a cire yayan kubewar a sanya su bushe sannan a nika har su zama gari sai a rinka sha da ruwa. Amma kada a sha ya wuce 5gm a rana.

 

Ana kuma yin tea da ganyen kubewa. (sources: information,com and pinterest.com)

Leave A Reply

Your email address will not be published.