GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Wata Budurwa Ramatu Tafida ‘Yar Shekaru 17 Ta Yanke Mazakutar Saurayin Da Zai Aureta a Jigawa

Wata Budurwa Ramatu Tafida 'Yar Shekaru 17 Ta Yanke Mazakutar Saurayin Da Zai Aureta a Jigawa

717

- Advertisement -

Wata budurwa mai suna Ramatu Tafida ‘yar shekaru 17 ta yanke mazakutar saurayinta mai shekaru 25 mai suna Abdulahi Sabo.

Wannan lamari dai ya faru ne a karamar hukumar Babura da ke jahar Jigawa.

 

Karanta: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Abia

 

Mai magana da yawun hukumar sibil difens ta jahar, AC Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar, inda ya ce da kyar suka ceci budurwar daga hannun mutanen da ke yunkurin lakada mata duka.

Ya ce Abdullahi dan asalin garin Garin Gabas, malamin Npower ne a karamar hukumar Babura, kuma ya riga ya kai kudi gidan su Ramatu da nufin zai aure ta.

 

Karanta: Hukumar INEC Ta Ce A Shirye Take Tsab Wajen Gudanar Da Babban Zaben Kasa

 

Da ta ke bayyana dalilin da ya sa ta aikata wannan aika aika, Ramatu ta ce sai bayan da Abdullahi ya yaudareta ya sadu da ita sannan ta ji labarin cewa ya na shirin fasa auren ya koma kan wata budurwar daban.

Ramatu ta ce sai da ta jira lokacin da za su kara saduwa tukunna ta tambaye shi idan wannan labari gaskiya ne, kuma bai musa ba.

 

Karanta: Amfanin Ganyen Kuka Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

Ta ci gaba da cewa, A nan ne ta fito da wukar da ta ke boye da ita, ta sare masa mazakuta.

An garzaya da Abdullahi asibitin Babura, inda daga nan aka tura shi asibitin Malam Aminu Kano.

 

Karanta: Samar Da Aiki: Gwamnatin Jihar Jigawa Zata Sake Gudunar Da Shirin Rabon Awaki

 

Ita kuwa Ramatu an gurfanar da ita a gaban kuliya, kuma ta na garkame har sai ranar 9 ga watan Satumba yayin da za a ci gaba da sauraran karar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.