GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Wata Sabuwar Kungiya Mai Ikirarin Wa’azin Musulunci Ta Bulla A Sokoto

Wata Sabuwar Kungiya Mai Ikirarin Wa’azin Musulunci Ta Bulla A Sokoto

44

- Advertisement -

Rahotanni sun bayyana cewa wata sabuwar kungiya da ke ikirarin wa’azin musulunci dauke da miyagun makamai, ta bulla a cikin jihar Sakoto daga jamhuriyyar Nijar.

 

Karanta wannan: Sarauniyar Kyau Ta Kasar Rasha Ta Musulunta, Ta Kuma Auri Sarkin Malaysia (Hotuna)

 

Kungiyar ta bulla ne a Watannin biyun da suka gabata inda ake zargin ‘ya’yan kungiyar sun soma bulla a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Tangaza kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai.

Mai shaidar wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce ‘ya’yan kungiyar na bin kauyuka suna karbar zakka daga masu abin hannu, kuma suna yin bulala ga mutanen da suka aikata abubuwan assha da suka sabawa dokokin addinin musulunci.

 

Karanta wannan: An Gano Gawar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Abaji

 

Mutumin ya shaida cewa ‘yan kungiyar sun fi mutum 200, kuma cikinsu akwai fulani da turawa da larabawa dauke da rawani da bindigogi.

“Suna bin gida-gida don karba kudade, mai rago zai bada naira dari biyu, mai kiwon sa kuma zai ba da naira dari biyar 2.

 

Karanta wannan: Tsoho Dan Shekaru 78 Ya Furta Kisan Mata 90 (Hotuna)

 

Mutumin ya kuma shaida cewa suna kai yara cikin daji, suna koya musu wasu abubuwa, idan

Leave A Reply

Your email address will not be published.