GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yadda ake Amfani Da Madara Wajen Magance Maikon Fuska

Yadda ake Amfani Da Madara Wajen Magance Maikon Fuska

631

- Advertisement -

Shan madara na kara lafiyar jiki, tana sanya fata ta rika sheki, ta sanya ta yi taushi da kuma santsi. Hakan ya sa a yau Mujallar Gulmawuya ta kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen magance yawan maikon fuska.

 

Karanta: Amfanin Aya 7 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

Abubuwan bukata

  • Madara
  • Gishiri
  • Ruwa
  • Auduga
  • Zuma

Milk&honey

Amfanin madara wajen magance maikon fuska

1. Madara na goge daudar fuska: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Daga nan a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.

 

Karanta: Cututtukan Da Tafasasshen Ruwan Albasa Ke Magancewa

 

2. Madara na sanya fata santsi: don haka za a iya amfani da ita a matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuska da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska, kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.

 

3. Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi: musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.

 

Karanta: Lauyan Atiku Bashi Da Lasisin Shiga Harkokin Shari’a a Najeriya – INEC

 

4. Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.