GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yadda Ake Cika Fom Din Neman Aikin Sojojin Ruwan Nijeriya (Nigerian Navy) A Yanar Gizo

Yadda Ake Cika Fom Din Neman Aikin Sojojin Ruwan Nijeriya (Nigerian Navy) A Yanar Gizo

37

- Advertisement -

 

Ku karanta hanyoyin da za ku bi wajen rajistar neman aikin Sojojin Ruwan Nijeriya. A nan za mu bayyana ma ku abubuwar ake bukata mai neman aikin ya mallaka, takardun da ake bukata sannan kuma yadda za ake rajistar.

Ga Abubuwan Da Ake Mutum Ke Bukatar Mutum Ya Mallaka Kafin Yayi Rajista:
 • Sai mutum ya kasance haifaffe sannan kuma dan asalin kasar Nijeriya ne kafin ya iya cika fom din neman aikin sojojin ruwa.
 • Mutum ya kasance kuma yana cikin koshin lafiya
 • Mutum ya kasance matashi ne tsakanin shekaru 18 zuwa 30 (wata sa’a a kan bukacin daga shekaru 18-26)
 • Wadand ke son rajista su kasance sun mallaki credit 5 a jarabawarsu ta NECO, ko GCE, ko kuma WASSCE amma dole da credit a kidaya (wato Mathematics) da kuma harshen turanci (English).
 • Mutum ya kasance ya cikin koshin lafiya ba tare da kowane rauni a jikinsa ba.
 • Mutum ya kasance ba shi da rikodin din ta’addanci.
 • Masu rajista su kasance marasa aure ne.
 • Maza kuma sai sun kasance da tsawaon akalla mita 1.65 zuwa 1.7 a tsayi.
 • Mata kuma tsayin su kada yayi kasa da mika 1.6.
 • Ya da kyau mutum ya san ilimin kwamfuta ko da kadan ni.
 • Duk wanda zai yi rajista kada ya kasance dan kungiyar sirri ne, ko mai shan miyagun kwayoyi.
 • Idan mutum fom din DSS zai cika ya kasance yana da takardar kammala NYSC

 

Karanta: Amfanin Aya 7 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

 

Abubuwar Kulawa Wajen Rajistar Neman Aikin Sojojin Ruwan Nijeriya
– Kada ka manta cika fom din kyauta ne. Ba sai ka kashe ko sisi wajen rajista amma idan a Cafe za’a yi ma ka dole sai masu cafe din sun dan karbi kudi daga hannun ka saboda yi ma ka rajistar da za su yi.

 

– Kada mutum ya biya ko sisi ga duk wani shafin yanar gizo da ta bukaci a biya kudi kafin yin rajista domin wannan ba shafin Rundunar Sojojin Ruwan Nijeirya bane, shafin ‘yan damfara ne.

 

Karanta: Wata Mata Ta Kona Mijinta Saboda Ya Ki Bata Lambar Bude Wayarshi

– Idan an fara daukar aiki, Rundunar sojojin ruwan Nijeriya ta kan bude shafin rajistar neman aikin, mutum zai iya bibiyar shafukar sadarwa na rundunar na Twitter, Instagram da kuma Facebook domin samun labari da karen haske akan lamarin rajistar.

 

 

Ga Yadda Ake Cika Fom Din Neman Aikin Sojojin Ruwan Nijeriya: 

– Mutum sai ya saukar da fom din DSSC dinsa wato download DSSC fom. Yin hakan sai mutum na bukata amma ba dole bane

 

– Mutum ya tabbatar da cewa an bude shafin rajista ba wai a kulle ya ke ba. Mutum zai iya rajista neman aikin a yanar gizo

 

Karanta: Uwar Jiki: Rigakafin Cutar Dajin Mahaifa (Womb Cancer)

 

– Idan mutum na so yayi rajistar neman aikin a yanar gizo, ya tabbatar da cewa yayi PRINTING (wato ya fitar da fom nasa) bayan ya cika fom din ya aikawa rundunar.
– Ka aikawa rundunar fom na ka bayan ka gama rajista idan za ka PRINTING ne.

 

– Sai mutum ya dan jira har sai Rundunar ta fitar da jerin sunayen mutanen da za ta tantance ta hanyar zuwa dubawa a shafinsu ta yanar gizo wato joinnigeriannavy domin duba suna.

– Mutum ya shirya da kayau wajen ganin cewa ya samu nasara wajen tantancewa da rundunar za ta yo.

 

Karanta: Manufofin Atiku Suna Da Hadari Ga Nijeriya – Shehu Sani

 

– Wadanda suka samu nasaran zuwa wajen tantancewa a harkar kiwon lafiya su suka samu nasaran isa tantancewar ta kashe kenan.

 

– Rundunar za su bukaci mutane su kai takardun ta asali wajen tantancewar.

A karshe dai

 

Wannan shine hanyoyin bi wajen yin rajistar neman aikin sojojin ruwan Nijeriya. Da fatan wannan jawabin yayi ma ku amfani.

Leave A Reply

Your email address will not be published.