GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yadda Ake Gullisuwa

Yadda Ake Gullisuwa

257

- Advertisement -

Barkanmu da sake saduwa a fannin girke-girkenmu. A yau darasinmu shine yadda za a hada gullisuwa a saukake.

Abubuwan hadawa

  1. Madara
  2. Sugar
  3. Ruwan dumi
  4. Man gyada
  5. Baking powder

Yadda ake hadawa

  1. ki samu bowl ki sa madara da baking powder kadan, Sai kuma sugar ( iya zakin da ki ke so).
  2. Ki sa ruwan kadan sai ki juya ki hade ya koma thick
  3. ki dinga diba ki na murzawa a hannunki ki kamar ball. Kina Dan iya sa Mai kadan a hannu. Ki samu saukin murzawa.
  4. A soya shi a cikin mai
  5. idan yayi golden brown sai a kwashe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.