GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yadda ake miyar kuka

Yadda ake miyar kuka

334

- Advertisement -

Abubuwan hadawa

 1. Garin kuka
 2. Nama ko kaza
 3. Attarugu
 4. Daddawa
 5. Manja
 6. Maggi da gishiri
 7. Kayan kamshi

 Yadda ake hadawa

 1. Ki daka daddawa ki hada da citta da masoro idan ta daku sai ki zuba attarugunki
 2. Ki ci gaba da dakawa har sai sunyi laushi.
 3. Daga nan kuma sai ki kwashe
 4. Ki dora tukunyarki a wuta ki zuba manja ki soya idan ya soyu dai ki zuba jajjagen ki aciki.
 5. Ki saka crayfish, maggi da gishiri ki rufe.
 6. Za kiga yana soyuwa, bayan ya soyu sai ki zuba ruwan naman ki aciki,  ki juya sai ki rufe zuwa minti biyar.
 7. Ki barshi har tsawon minti biyar ya ta tafasa.
 8. Da ga nan sai ki kada ta ki dinga zuba kukarki a hankali, kina burgawa har tayi kaurin da kike bukata. Ok kuma zuba naman ki aciki
 9. Sai ki kuma rufeta zuwa minti biyar sai ki sauke.

Leave A Reply

Your email address will not be published.