GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yadda Za Ku Magance Warin Baki Ta Hanya Mai Sauki

Yadda Za Ku Magance Warin Baki Ta Hanya Mai Sauki

53

- Advertisement -

Warin baki, musamman a wannan lokaci na azumi, abu ne da za ka same shi a tare da mutane da dama har da wadanda ma ba ka zaci samunsu da warin bakin ba.

 

Karanta: Baba Buhari Yawon Ya Isa Haka Na – Rokon Rahma Abdulmajid

 

Warin bakin mai azumi kuwa yana da alaka ne da rashin ci da sha da yawan surutu da ake yi a tsawon yini, wanda hakan ke jawo baki ya kasance a rufe a mafi yawan lokuta.

Tabattar da cewa baki baya wari shi kansa kwalliya ne, domin dai duk yadda mutum ya kai ga kyau idan har yana magana kuma ana jin warin bakinsa akwai babbar damuwa.

Yana da kyau a kula da yadda ake wanke baki da hakora da kuma harshe, domin idan daya daga cikinsu bai wanku ba, hakan zai iya haifar da warin baki. Yawan cin tafarnuwa da albasa da kuma shan giya na haifar da warin baki.

Karanta wannan: Abinci 5 Da Ke Kara Ingancin Barci

Ga wasu hanyoyi masu sauki da za ka bi don magance warin baki:

  •  Idan ana sanye da hakorin roba ne, yana da kyau a rika wanke su sannan a cire su a baki a lokacin da za a kwanta bacci da dare. Kwanciya da su a baki na haifar da cututtuka da ke sanya warin baki.
  •  A yawaita shan ruwa sosai; shan ruwa na wanke kowace datti da ke baki. Yana da kyau a rika kurkura bakin da zarar an tashi bacci, domin fitar da kowace dauda da ke cushe a tsakanin hakora.
  •  Idan an san ana da warin baki, a kasance cikin wanke baki da magogi hade da man goge baki a duk lokacin da aka gama cin abinci domin magance matsalar wari.
  •  Amfani da burushi daya na tsawon lokaci yana haifar da warin baki. Don haka, yana da kyau a rika canza magogi bayan watanni biyu zuwa uku, domin samun hakora masu lafiya.
  • Kada a manta zuwa ganin likitan hakora, domin ya taimaka wajen wanke hakoran da magunguna domin rage warin baki.
  •  A yawaita cin kanamfari sosai, cin kanamfari na magance kwayoyin cututtukan da ke haifar da warin baki.
  • Yawan cin ‘ya’yan itatuwa kamar su amfuna da lemu da mangoro da abarba da dai makamantansu na rage warin baki
  • A samu garin ‘baking soda’ sannan a kwaba da ruwa sai a rika Kurkure bakin da shi, amma kada a hadiye. Za a iya samun ‘baking soda’ a shagunan da ke sayar da kayakin hadin ket.

Leave A Reply

Your email address will not be published.